KATSINA: Yadda ’Yan Sanda su ka kama gaggan masu safarar muggan makamai daga Jamhuriyar Nijar

0

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta bayyana samun wata gagarimar nasarar damke wasu rikakkun masu safarar muggan makamai daga Jamhuriyar Nijar, zuwa cikin Najeriya.

An damke Haruna Yusuf da ‘ya’yan sa biyu, bisa zargin sana’ar garkuwa da mutane da kuma dillancin muggan makamai.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Katsina, Sanusi Buba, ya bayyana cewa Yusuf mai shekaru 47, mazaunin kauyen Muduru ne cikin Karamar Hukumar Mani ta Jihar Katsina.

Ya ce shi ne ke jagorancin safarar manyan makamai daga Jamhuriyar Nijar, su na jigilar su zuwa cikin Najeriya zuwa jihohin Katsina da kuma Zamfara.

Buba yace an kama wanda ake zargin tare da ‘ya’yan sa biyu, Salisu mai shekaru 20 da kuma Shuaibu mai shekaru 18.

Sauran wadanda ake zargi sun hada Haruna Yusuf, wanda ke kauyen Sawarya cikin Karamar Hukumar Kaita, Haruna Adamu, Auwal Abubakar duk a cikin garin Muduru.

Kwamishinan ‘yan sandan ya kara da cewa Yusuf ya fada da bakin sa cewa su na shigo da muggan makaman ne daga Jamhuriyar Nijar ga wani mai suna Lawan Zayyana, Haruna Adamu da Auwal Abubakar, su kuma su na kai wa ‘yan bindiga.

“Ya ce ya saida akalla bindigogi da albarusai za su kai 10,000 ga masu garkuwa da mutane a cikin dazuka.

“Sannan kuma Haruna Adamu da Auwal Abubakar da kan su sun bayyana mana yadda su ka rika karakainar jigilar kai wa masu garkuwa muggan makamai da tulin albarusai a Gurbi da Dan-Magaji duk a cikin Jihar Zamfara.” Inji Kwamishinan ‘Yan sanda Buba.

Sauran Gungun Mugun Iri:

Sauran wadanda jami’an tsaro su ka nuna wa manema labarai sun hada Murtala Haruna, wanda dan uwan dillalin bindigogin ne, sai Ibrahim Dabo da ke kauyen Natsinta, Kandamau, Maradi da ce cikin Jamhuriyar Nijar.

Akwai kuma Sambo Muhammadu da Jibrin Adamu, dukkan su masu shekaru 20 kowanen su.

Akwai kuma Sani Ibrahim, Yusufa Muhammadu, Abubakar Muhammadu, Abdullahi Dabo, Murtala Ado, Sani Muhammdu, Umar Bello dukkan su a kauyen Natsinta cikin Kandamau da ke Jihar Maradi ta Jamhuriyar Nijar.

An kuma kamo Basiru Usman da ke kauyen Tsanni cikin Karamar Hukumar Batagarawa, shi ma dan uwan babban dillalin muggan makaman da kuma Zayyana da Kamarudini Jafaru a Muduru cikin Karamar Hukumar Mani a Jihar Katsina.

An dai samu muggan makamai da babura bakwai a hannun su.

Share.

game da Author