A wata ziyara da Ministan Sadarwa Isa Pantami ya ce sun wakilci Gwamnatin Tarayya zuwa Sokoto domin jajantawa da duba yawan barnar da gobara ta yi, Ministan ya nuna matukar damuwa ganin irin gagarimar barnar da gobarar ta yi a babbar kasuwar Sokoto.
Pantami ya bayyana haka a shafin san a Facebook, tare da wallafa wasu hotuna masu dauke da irin mummunar barnar da gobarar ta yi.
Cikin jawabin sa da aka buga a shafin na sa, ministan y ace, “A yau mun wakilci Gwamnatin Tarayya zuwa Jihar Sokoto don jaje da kuma binciken girman barna da wuta ta yi a kasuwar, domin gwamnatin tarayya ta taimaka wajen gyaran kasuwar da kuma taimaka wa ’yan kasuwa.
“Hakika abin da idon mu ya gani akwai abin tausayi. Domin bisa ga jawabin Gwamnan Jiha, Aminu Tambuwal, kusan kashi 60 cikin 100 na kasuwa mai shaguna manya da kanana kimanin guda 16,000 duk sun kone.
“Mun jajanta wa ’yan kasuwa, Gwamna da kuma shugaban mu baban mu Sarkin Musulmi a matsayin mu wakilan Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari.”
Minsta Pantami wanda ya kai ziyarar jajen tare da sauran ’yan tawagar Gwamnatin Tarayya. Sun ziyarci cikin kasuwar, kuma ya yi addu’ar Allah ya kiyaye na gaba.