Ofishin Huldar Cinikayya da Kasashen Waje na Najeriya (NOTN), ya nuna cewa Najeriya ta shigo da kaya daga kasashen Chana da Amurka da Indiya a cikin watanni shida na farkon shekarar 2020.
Tsakanin Afrilu zuwa Yunin 2020 Najeriya ta shigo da kaya na naira tiriliyan 6.2 wato kasa da kashi har 27.30 na adadin kudin kayan da aka sawo daga kasashen waje tsakanin Janairu zuwa Maris, 2020 kafin a kulle kasashen duniya sakamakon cutar korona.
Sai dai kuma ita Najeriya a wannan watannin ba a sayi kayan ta an fita da su waje da yawa ba.
Hukumar ta ce kayan naira tiriliyan 2.2 kacal aka saya aka fitar da shi daga Najeriya, kusan rabin adadin kudaden da aka yi ciniki a watanni uku na farkon shekarar 2020 kenan.
Hakan kuwa na nuni da cewa an samu gibi har na naira tiriliyan 1.8 a cikin watanni uku kacal kenan.
“Kusan rasbin kayan da aka shigo da su Najeriya, duk daga nahiyar Asiya aka sayo su. Musamman saboda China da Indiya su suka ja kudaden kashi 39.32 na adadin kayan da aka shigo da su Najeiya a tsakanin watannin Afilu, Mayu da Yuni, 2020.” Kama yadda rahoton ya nuna.
Kusan kashi 31.41 na kayan da aka shigo da su a watannin Afrilu zuwa Yuni, daga Chana aka shigo da su. Wato cinikin naira tiriliyan 1.2 duk daga Chana a cikin watanni uku kenan.
Sauran kasahen sun hada da Amurka inda aka shigo da kayan naira bilyan 428.9.
“Indiya da Netherlands da Jamus su ne na uku, na hudu da na biya, sai kuma Bazil, Rasha, Koriya ta Kudu da Birtaniya da Italy.
Discussion about this post