Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakin sa Yemi Osinbajo za su kashe naira bilyan 3.4 daga cikin kasafin 2021 a ciye-ciye da tafiye-tafiye.
Yayin da Buhari ya amince da kashe wa kan sa naira bilyan 2.6, shi kuma Osinbajo naira milyan 873 ne za a kashe wa ofishin sa.
Kamar yadda su ka rika gabza wa ofisoshin na su kudi tsawon shekaru biyar a jere, wannan shekarar ma ba ta canja zani ba. PREMIUM TIMES ta bibiyi yadda shugaban da mataimakin sa su ka dumbuza wa kan su kudade a wannan shekarar.
Kamar yadda za su kashe a wannan shekarar, hakan ne dai su ka rubuta wa kan su a shekarar da ta gabata, duk kuwa da cewa korona ba ta bari su biyun sun yi zirga-zirga kasashen waje ba.
Cikin 2019 Buhari ya lashe naira biyan 1.5 wajen abinci da tafiye-tafiye, naira bilyan 1.52 cikin 2018, cikin 2017 kuma naira bilyan 1.45, sai cikin 2016 naira bilyan 1.43.
A zirga-zirga kuwa cikin naira bilyan 2.4: Daga kudaden za a kashe naira milyan 775.6 a tafiye-tafiyen cikin gida, sai kuma naira biyan 1.7 a tafiye-tafiyen kasashen waje.
Shi kuwa Osinbajo zai kashe naira milyan 801 a tafiye-tafiye, inda daga ciki naira milyan 284 zai kashe zirga-zirgar cikin gida. Ta kasashen waje kuwa naira milyan 517.1
Ciye-ciye, tande-tande da lashe-lashe:
Ofishin Buhari da na Osinbajo sun ware naira milyan 195.5, sai kuma iyalan Buhari naira milyan 124.
Kusan haka ne aka kashe masu cikin 2017 da 2016, amma bambancin ba wani mai yawa ba ne.
Ofishin Buhari an ware naira milyan 25.7 domin sayen lemuka da kayan sha.
Kamar yadda aka kashe wa ofishin Osinbajo naira milyan 71.5 a 2020, hakan za a sake kashewa a 2021.
Abinci za a kashe wa naira milyan 50.9, sai shaye-shaye naira milyan 18.3 sai gas da fetur naira milyan 2.4.