KANAWA SUN SHIGA TASKU: An kara gano yara bakwai da aka sace a Kano can a garin Enugu

0

Iyayen yaran da aka gano din sun ce har yanzu su na cigiyar yaro 113 da aka sace a Kano, har yau babu abari.

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa wasu yara bakwai da aka bada cigiyar an sace su, an gano su a garin Enugu ta jihar Anambra.

Kwamishinan Yada Labarai na Kano Muhammad Garba, ya ce tuni har iyayen yaran sun gane ‘ya’yan su, kuma nan gaba kadan gwamnatin Kano za ta damka yaran a hannun iyayen su.

Ya yi wannan magana ce a ranar Litinin, lokacin da ya kai ziyasa gidan marayu a Kano.

Ya ce kwamitin da gwamnatin Kano ta kafa ne domin bincike ya gano yaran can a Enugu.

PREMIUM TIMES a cikin 2019 ta buga labarin yadda aka saci yara tara a Kano, aka rika sayar da su a Anacha bayana an canja masu suna a jihar Anambra.

Bayan an ceto yaran ne shi kuma Kwamishinan Yan sanda na Kano ya damka su a hannun iyayen su, a gaban manema labarai.

Iliyasu ya ce jami’an sa sun damke mutum takwas da ke da hannu wajen sata da safarar yaran kanana.

Ya ce mutanen sun shahara wajen safarar kananan yaran da su ka sace daga Kano zuwa jihar Anambra.

Ya ce jami’an tsaro sun yi wani gagarimin samame bayan da iyayen wadanda aka sace suka shafe shekaru biyarsu na kuka.

Shugaban Kungiyar Iyayen Yaran da aka Sace, Isma’el Isma’el ya nuna farin cikinn gano wadannan kananan yara da aka yi.

Sai dain ya ce har yanzu ana neman yaro 113.

Share.

game da Author