Duk da cewa an kwashe shekaru hudu zuwa biyar ana markabu tsakanin kamfanin Intels da Gwamnatin Tarayya, wanda hakan Atiku Abubakar ya ce shi ne sanadiyyar sayar da hannayen jarin sa da ga Intels, kamfanin ya fito ya karyata Atiku cewa babu wata takun-saka tsakanin Intels da gwamnatin Buhari.
Cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar bayan da Atiku ya bayyana dalilin ficewar sa gaba daya daga kamfanin, Intels ya wata ’yar tangardar gudanar da tsar ice aka samu da gwamnati, amma kuma ana kan warware ta.
Kakakin Yada Labarai na Intels, Tommaso Ruffinoni, ya bayyana cewa a kowane lokacin Intels na gudanar da kasuwanci sa bisa tsari.
Sai ya ce Atiku ya kwashe hannayen jarin sa ya fice ne saboda ba ya iya jure sabbin tsare-tsaren tafiyar da tattallin arzikin kamfanin na Intels.
Shekaru 17 kenan Intels na gudanar da ayyukan sa a manyan tashoshin ruwan Najeriya.
Sai dai kuma bayan hawan Shugaba Muhammadu Buhari, an samu sabani da Intels har aka soke kwangilolin da ake bai wa kamfanin tsawon shekaru da dama.
Duk da haka dai kamfanin a yanzu ya ce babu wata takun-saka tsakanin sa da gwamnatin Buhari.
Akitu ya saida hannayen jarin sa a kamfanin Intels, ya ce Buhari ke neman karya shi.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga rahoton yadda Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya sayar da dukkan hannayen jarin sa a kamfanin Intels.
Atiku wanda ya fara sayar da hannayen jarin a hankula tun shekarun baya, ya bayyana cewa ya yi hakan ne saboda tun farkon hawa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari aka dauki tsauraran matakan sai an karya shi.
Wata sanarwa da kakakin yada labarai na Atiku, wato Paul Ibe ya fitar a ranar Litinin, Atiku ya ce ya yanke shawarar sayar da hannayen jarin sa kakaf a kamfanin Intels, saboda gwamnatin Buhari ta rugurguza tattalin arzikin Najeriya.
“Tunanin ya zo ne saboda tun shekaru biyar da su ka gabata Gwamnati ta rika bugun-kirjin sai ta karya harkar kasuwancin Intels, kamfanin da ya dauki dubban ma’aikata aiki. Kuma duk wannan karya kamfanin da ta yi, saboda dalilai ne kawai na siyasa.”
Atiku wanda ya yi mataimakin shugaban kasa tsakanin 1999 zuwa 2007, kuma ya yi takarar shugaban kasa tare da Buhari cikin 2019, ya ce kamata ya yi a ce batun siyasa badan, haka batun harkar kasuwanci kuma ita ma daban.
Atiku ya ce ya karkata kudin hannayen jarin sa daga Intels zuwa wasu harkokin kasuwancin da za su samar wa dimbin jama’a ayyukan yi a kasar nan.