Jami’ar Maryam Abacha tare da haɗin guiwar gidauniyar AAG-Foundation, ta baiwa jami’ar Bayero dake Kano Kyautar motocin daukar ɗalibai 60.
Hakan na daga cikin wani shiri na tallafawa harkar Ilimi a wannan yanki na Afrika da jami’au MAAUN keyi tare da hadin gidauniyar gidauniyar AAG.
Shugaban jam’iyyar BUK, Farfesa Sagir Ahmed ya karɓi mukullan motocin daga hannun jami’in jami’ar Maryam Abacha Dakta Bala Muhammad a harabar jami’ar BUK dake Kano ranar Talata.
Da yake jawabi yayin gabatar da mukullai da takardun moticin, Dakta Muhammad ya ce karimcin ya yi daidai da hangen nesan MAAUN da gidauniyar AAG na samar da ci gaba mai dorewa cikin sauki ga kowa da kowa a fannin ilimi.
Ya kara da cewa an kuma bayar da gudummawar ne don tabbatar da tsarin sufuri ba tare da matsala ba da kuma kau da cinkoso wanda hakan zai da hana yaduwar cutar Korona a cikin jami’o’in Najeriya.
Dakta Muhammad ya kara da cewa “Manufar bayar da gudummawar ita ce bayar da gudummawa ga kokarin da jami’ar ke yi na samar da tsarin sufuri ba tare da matsala ba don samun ingantaccen ilmi da kuma taimakawa wajen yakar cutar Korona da rage cunkoso.
A karshe mataimakin Shugaban Jami’ar BUK ya yaba wa Farfesa Adamu Gwarzo bisa wannan karimci na ci gaba da tallafa wa jami’ar da ya ke yi. Sannan kuma yace Jami’ar za ta yi amfani da motocin yadda ya kamata, yana mai cewa hakan zai taimaka sosai wajen rage wahalhalun da dalibai ke sha a fannin sufuri.
Discussion about this post