Jami’an tsaro sun damke wasu matasa 5 da suka kashe wani matashin makiyayi a lokacin da yake kiwo a yankin gundumar Atyap, Karamar Hukumar Zangon Kataf, dake jihar Kaduna.
A wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun sanar wa gwamnatin jihar cewa sun damke uku daga cikin wadanda suka kashe wani makiyayi ranar Lahadi, sannan sun kamo sauran biyu ranar Litinin da safe.
” Bayan jami’an tsaro sun samu labarin wani makiyayi ya bi ta gonar wani har ana zargin sa da barnata wani sashe na gonar, sai suka gaggauta garzaya wannan gona. Saidai kuma isar su ke da wuya sai suka ci karo da gwar makiyayin kwance malemale cikin jini har an kashe shi.
” Bayan bincike da jami’an tsaro suka yi sun kama wasu mutum uku daga cikin wadanda suka kashe wannan makiyayi, David Kure, Peter Adamu da Bulus Duniya. Ranar lilinin kuma suka kama sauran mutum biyu, Matthew Peter da Yohanna Chawai.
Aruwan ya ce yanzu haka ana ci gaba da tuhumar wadannan samari, kafin a gurfanar da su.