Jami’an tsaro a jihar Katsina sun ceto mutum 103 da aka yi garkuwan da su a jihar.
Gwamnan jihar Aminu Masari ya sanar da haka da yake yi wa wadanda aka yi garkuwar da su huduba a fadar gwamnati a garin Katsina.
“Ceto wadannan mutane na daga cikin kokarin gwamnati na ganin an inganta tsaro da gwamnati ke yi a jihar. Mun samu madafa wanda zai taimaka wajen ceto rayukan mutanen da aka yi garkuwan da su sannan kuma da hana yin garkuwa da mutane da aikata miyagun aiyukka a jihar.
“Muna aiki ne da sojoji, DSS, ‘yan sanda, sojojin sama kuma ina so in sanar muku cewa tun daga daliban makarantar sakandaren Kankara da aka yi garkuwan da su zuwa wadannan mutane babu wanda aka biya kudin diya a kansa.
Masari ya hori mutanen da aka ceto daga masu garkuwa da mutane maida al’amuransu ga Allah, su ga haka a matsayin jarabawa ce daga Allah.
Daga cikin wadanda aka yi garkuwar da su akwai mata masu shayarwa, ‘yan mata masu shekaru 6 zuwa 16, tsoho mai shekara 70, soja daya da dan sanda daya.
Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Boko Haram suka sace daliban makarantan Kankara su 333 a garin kankara a cikin shekarar 2020.
Sai da suka dauki tsawon awa 5 cur suna kwashe yaran makarantan a cikin kankara kafin suka tafi da su.
Bayan haka Masari ya bayyana yadda Suka ceto wadannan yara inda yana mai cewa sun hada da jami’an tsaro da wasu jami’an gwamnati wajen tattaunawa da masu garkuwan har aka iya ceto su.
Sannan kuma ko sisi gwamnati bata ba su ba, tattaunawa ta yi da su har aka cimma matsaya suka saki yaran.
Masari ya kara da cewa ba Boko Haram bane suka sace yaran, yan bindiga ne tsangwararan suka tafi da yaran cikin daji.