Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da wani labari da ake yadawa wai ta na daukar mutane aiki.
Festus Okoye, Babban Kwamishina kuma Shugaban Yada Labarai da Wayar da kan Masu Zabe na hukumar, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya bayar a ranar Juma’a a Abuja.
Okoye ya ce a yanzu dai INEC ba ta aukar kowa aiki, ya kara da cewa tun tuni aka dakatar da daukar sabbin gama jami’a da wararrun ma’aikata.
Ya ce: “INEC na so ta kara jawo hankalin jama’a zuwa ga aikin da wasu jami’an karya ‘yan damfara su ke yi na aukar aiki na jabu.
“’Yan damfarar sun bue gidajen yana na karyar daukar aiki inda su ke karbar kudade a hannun jama’ar da ba su ankara ba har su na ba su takardun kama aiki na bogi da sunan hukumar.
“Idan za a iya tunawa, tun a ranar 30 ga Mayu, 2020, Hukumar ta bada wata sanarwa inda ta ja hankalin jama’a kan yaduwar wasu takardun kama aiki na karya da aka ce wai sun fito daga gare ta ne.
“Mun sanar da jama’a lokacin cewa Hukumar ta dakatar da shirin ta na daukar ma’aikata.
“Mun shawarci kowa da kowa da ya yi watsi da duk wata ji-ta-ji-ta game da daukar aiki da raba takardun kama aiki da aka ce wai daga Hukumar ne su ka fito, kuma mun sanar da hukumomin tsaro wannan damfarar.”
Okoye ya ce wannan Hukuma dai amanar jama’a ce wadda ke gudanar da aikin ta a bisa tsarin da aka amince da shi na aiki tsakani da Allah kuma a bayyane.
Ya ce wannan tsari na yin aiki a bayyane shi ya sanya a duk lokacin da hukumar ke daukar ma’aika ake yayatawa.
Okoye ya ce, “Mu an kara jan hankalin jama’a da su san dabarun da ‘yan damfara ke amfani da su don kada su fada cikin tarkon su na masu aikata laifi.”