Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta koka da yawan gine-ginen da aka yi watsi da su a tsakiyar garin na Abuja.
Daraktan sashin sanya ido da dubawa, Olawale Labiyi, wanda Obinna Nkwocha na sashin lura da birni ya wakilta, ya bayyana hakan a lokacin da suka kai ziyarar gani da ido ranar Laraba a cikin garin Abuja.
Labiyi ya ce gine-ginen da aka yi watsi da su na da hadari ga tsaro saboda za su iya zama maboyar ‘yan daba da masu aikata laifi.
Ya yi kira ga mazauna yankin da su kasance masu lura a koda yaushe kuma su kai rahoton duk wani motsin da ba su yarda da shi ba a gine-ginen dake makwabtaka da su.
Labiyi ya umarci sashen dake kula da tabbatar da an kammala gone-gine da su tabbatar da cewa babu wani gini ko gini da aka barshi babu kowa.
Ya kuma shawarce su da su yi aiki da tabbatar da an bi komai bisa doka domin kauce wa fadawa tarkon wadanda za su iya kai kara kotu ba tare da hujjoji ba.
A karshe Labiyi ya yaba wa Sakatarorin FCTA, sassan da kuma hukumomin (SDAs) saboda tabbatar da ayyuka sun ci gaba yadda aya kamata musamman a lokacin hutun kwananan da aka yi.
Discussion about this post