Hisba ta kama matasa 53 da ke ta’ammali da muggan kwayoyi a Kano

0

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Hisba dake jihar Kano Lawal Ibrahim ya sanar da kama wasu matasa 53 da aka samu suna ta’ammali da muggan Kawayoyi sannan kuma da muzguna wa mutane haka kawai.

Ibrahim ya ce hukumar ta kama wadannan matasa a Lamido Crescent dake karamar hukumar Nasarawa bayan wasu mutanen sun kawo karar ta’addancin da wadannan matasa ke aikata a wannan unguwa.

Ya ce an kama wadannan matasa da laifin siyar wa da ta’ammali da muggan kwayoyi a unguwar.

Daga cikin wadanda aka kama akwai maza 27 da mata 26 kuma duk basu wuce ‘yan shekara 17 zuwa 19 ba.

” Binciken da aka gudanar ya nuna cewa wannan shine karon farko da wadannan matasa ke aikata irin wannan laifi.

“A dalilin haka ya sa muka ja musu kunne da yi musu hudubar zama mutane na gari.

” Bayan haka mun sake su domin su koma gida wajen iyayen su.

Shugaban hukumar ya hori matasan jihar da su nisanta kansu daga aikata munanan aiyuka, su zama mutane na gari.

A watan Disamba PREMIUMTIMES ta buga labarin yadda hukumar ta kama wasu bata gari 43 da aka samu suna aikata laifuka dabam-dabam a jihar.

Ma’aikata sun damke wadannan masu laifuka ne a Kasuwar Kwanar Gafan, dake karamar hukumar Garun Malam, dame jihar.

Kwamandan rundunar Hisbah Harun Ibn-Syna ya bayyana cewa 34 daga cikin wadanda aka kama, mata ne sauran maza.

Share.

game da Author