Shekarun Janet Olaleye 60 a duniya, kuma ta na da yara uku. Mace ce mai himmar noma, kuma sana’ar noman ya na rufa mata asiri, kamar yadda za ku ji bayanan da ta yi wa PREMIUM TIMES, a wannan tattaunawa da mata manoma, kashi na 11.
PT: Ke noman me da me ki ke yi ne?
JANET: Ni man ja na ke nomawa, sana’ar tatsar manja ne keyi, kuma ina da injinan da na ke matsar manja din da su. Sannan kuma ina yin ci-da-karfi, wanda a ke yi da hannu.
An tambaye ta shekara nawa kenan ta na noman kakwar manja, sai Janet ta ce ta kai shekara 10, kuma da kudin ta ta sayi gona, sai kuma wadda ta gada a wajen iyayen ta.
Sai dai kuma ta bayyana cewa ba ta san iyakar fadin gonakin ta ba, amma dai a kiyasin da ta yi, ta ce za su iya kaiwa hekata 10.
Janet da ce daga Hukumar NIHORT ta ke samun irin shukawa, amma wasu lokuta ta kan samu daga Ma’aikatar Gona.
“Na zabi sana’ar noman man ja da tace shi da matsar sa saboda tun ina karamar yarinya na ke lura da irin yadda mahaifiya ta ke yin sana’ar noman man ja din.
“To a lokacin a gaskiya a gargajiyance su ke matsar man ja, ni kuma da na kama sana’ar, sai na ce bari na tsaftace yadda ake matsar man ja din nan a zamanance kuma.
“A wancan lokaci na baya duk da guyawun mu mu ke wahalar aikin kwakwar man ja. Amma zamanantar da harkar ya kawo sauki a yanzu sosai.
Janet ta ce ta na shuka irin zamani ne, kamar yadda gwamnatin ke wayar da kan jama’a a rika yi domin samun bunkasar amfanin gona.
“Mun yi gamo da katarin samun na’uro’in aikin man ja na zamani ne a karkashin Kungiyar Kananan Manoma Mata, wanda Hukumar SMEDAN ta ba mu ramcen kudade da kuma tallafin da mu ka yi amfani kudaden mu ka sayo kayan aikin.
Janet ta ce ramcen naira milyan biyu aka ba su, su ka sayo injinan aiki.
“Ni yanzu wannan noma da sana’a ta karbe ni sosai. Domin a kullu na kan tara ruwan man ja har duro 15, a kowane sati na kan tara duro 105. Ka ga a kowane wata ina tara duro 420 kenan.”
Ta ce a da can baya sai sun dauka sun kai kasuwa sannan su sayar. Amma yanzu kuwa akwai mutanen da ke zuwa garin su daga Lagos da Ibadan su na sari, su kai can su sayar.
Ta kara da cewa ta taba samun tallafi daga gwamnatin jiha, amma ba ta taba samu daga gwamnatin tarayya ba.
“Ni a inda na ke noma da sana’ar man ja, ba ni samun wani nuna bambanci daga maza masu irin wannan sana’a.
“Kuma ni ce shugabar wannan sana’a a wannan jihar ta mu. Ka ga babu wani wanda zai zo ya yi min uwa-makarbiya, har ya shiga gaba na.
“Babbar matsala da kalubale bai wuce rashin kudi ba. Injinan da mu ke amfani da su masu tsada ne. To kuma ita wannan sana’a, yawan injinan da ka ke amfani, to yawan abinda da za ka iya tatsa kenan na man ja. Wato iyar kudin ka, iyar shagalin ka.”
A karshe ta yi kira gwamnati ta taimaka masu, domin a lokacin kullen cutar korona sun dibga babbar asara, kuma har yanzu ba su gama farfadowa ba.
Discussion about this post