HIMMA DAI MATA MANOMA: Takin zamani shi ne takaicin da mu ke fama da shi – Fatima

0

Wata mata mai shekaru 64 mai suna Fatima Bello, ta yi korafin cewa babban takaicin su wajen kokarin bunkasa harkokin noman su, shi ne rashin samun isasshen takin zamani.

Sai dai kuma ba a nan ta tsaya ba, Fatima ta kara da cewa ya kamata gwamnati ta tallafa wa mata manoma ta hanyoyi da dabarun horaswa da ilmantar da su hanyoyin bunkasa noman da kuma kayan aikin noma na zamani.

Fatima mace ce da ta maida mai hankali ga noma a jihohin Sokoto da kuma Kebbi.

A zaman tattaunawar ta inda ta bai wa PREMIUM TIMES labarin rayuwar ta a matsayin mai noma, ta ce ta yi karatu a Makarantar Horon Jinya da Unguwar Zoma ta Sokoto, sannan kuma ta na da Difiloma a fannin koyarwa. Daga baya ta shiga Makarantar Koyon Fasahar Kiwon Lafiya.

Fatima ita ce mace ta takwas mai himmar noma da aka tattauna da ita.

Duk da ta dade a duniya, ta ce ba ta wuce shekaru uku da shiga harkar noma tsundun ba. Sannan kuma ta ce shinkafa da gero da wake kadai ta ke nomawa.

“Na fara noma bayan na gaji gonaki biyu a daga mahaifi na. To dama kuma akwai wani suriki na da ke yawan ba ni shawara cewa na shiga harkar noma. Shi ya dade ya na noma, tsawon shekaru 40. Kuma ya na da digiri a fannin noma. To yayin da na gaji wadannan gonaki, sai na shiga noma gadan-gadan.

“Ka ga abin takaici akwai mata da yawa a yankin mu wadanda sun gaji gonaki daga iyayen su ko mazan su. Amma ba su da sha’awar noma ko kuma sukunin yin noman. To da gwamnati ta shigo ta na bayar da tallafi, sai na rika jawo wadancan mata a jika, inda na kafa kungiyar mata manoma. Saboda ita gwamnati ba ta ware mutum daya ta ba shi, sai dai kungiya.

“Ni gona ta ba ta wuce hekta biyu ba. A tawa gonar wake kadai na ke nomawa. Amma akwai ginar suriki na da ke hannu na, wadda na ke shuka gero da shinkafa. Jimla sun kai hekta biyar kenan.

Fatima ta ce a kasuwa ta ke zuwa ta sayo irin da ta ke shukawa. Amma surikin ta ne ke ba ta irin shinkafar da ta ke shukawa.

“Amma ina shuka geron da Ma’aikatar Gona ke sayarwa, wanda wani dan uwa na ne ya kawo min shi. Ta hanyar san a samu geron, saboda ba za ka taba ganin ana sayar da shi a kasuwa ba.

Sannan ta ce ta na amfani da kayan noma wajen hudar shinkafa, amma a wajen gero, matasa majiya karfi ta ke daukowa su yi mata noma.

Ta ce surikin ta ke da kayan noman, sai dai kawai ta dauko hayar direban da zai yi mata hudar ta biya shi.

“Na kan noma buhun shinkafa 68. Gero kuma a karamar gona na kan noma buhu 20 a babbar kuma buhu 30.

A harkar noman shinkafa na fara da jarin naira 500,000. A karamar gonar da na ke noma gero kuma na fara da jarin 60,000. A babbar kuma da naira 400,000.

“Idan ka fara noman shinkafa da rani tilas ka tanadi kudi da yawa, saboda sai ka rika tanadar wa shinkafar ruwa. Wannan ne zai maka kudi sosai. Tilas sai ka sayi famfon ban-ruwa da kuma janareton janyo ruwa.

“Babbar matsalar mu dai takin zamani, saboda ba a samu a hannun gwamnati kai-tsaye. Sai dai na bai wa suriki na ya sayo min a kasuwa kan naira 15,000 duk buhu daya. Saboda haka idan ta kuke na rasa takin zamani, sai dai nay i amfani da takin gargajiya, wato takin dabbobi.

“Sannan wani abin takaici, shi ma takin zamanin a yanzu ya yi tsada, saboda kowa ya san ana bukatar sa idan takin zamani ya gagari manomi.

Yayin da ta ce ba ta wani da-na-sani a harkar noma, sai dai kuma ta bayyana cewa ta sha fama da makiyaya, wadanda ke kiwo kusa da gonar da wani dan ta ke noma.

“Saboda rashin mutuncin wadannan makiyaya ya sa ni ba ni ma yin noma a wajen. Sai su bari amfanin gonar ka ya yi yabanya, sannan su banka shanu a ciki, su cinye kakaf.

A kungiyance, Fatima ta ce ta na mu’amala da SWOFAN, wato Kungiyar Kananan Manoma Mata ta Najeriya.

Share.

game da Author