HIMMA DAI MANOMA MATA: Karancin kudade da tsadar takin zamani ne cikas din bunkasa noma ga mata – Sabuwa Jigawa

0

Sabuwa Muhammad, wata mai noma ce a Jihar Jigawa. Duk da ta na da yara uku a gaban ta, hakan bai hana ta himmar noma ba.

A bangaren karatun zamani, har difiloma gare ta a Kwalejin Noma ta Binyaminu Usman da ke Hadejia.

Sabuwa mai shekaru 42, ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ta na da sha’awar noma sosai.

A wannan tattaunawa da aka yi da ita, ta bayyana wa wakilin mu, Sabuwa ta bayyana matsalar karancin kudade da karanci ko tsadar takin zamani ne babban kaicon su.

PT: Wadanne irin kayan gona ki ke nomawa?

Sabuwa: Ina noma gero, dawa, gyada da shinkafa.

PT: Shekara nawa kenan ki ke sana’ar noma?

Sabuwa: Na shafe shekaru 12 kenan ina sana’ar noma.

PT: Banda sana’ar noma, ko ki na wata sana’a kuwa?

Sabuwa: Ina yin kiwon kaji kuma ina da wurin da na ke sana’ar sarrafaawa ko tashar man gyada.

PT: Ya maganar yadda ki ke samun gonakin da ki ke nomawa kuwa?

Sabuwa: Ba ni da wasu gonaki kuma ba ni karbar aro ko jingina a hannun kowa. Gonakin da na ke nomawa na miji na ne.

PT: Ko gonar ta na da girma kuwa?

Sabuwa: Ba ta wuce hekta biyu ba kadai.

PT: Ta yaya ki ke zaben irin da ki ke shukawa?

Sabuwa: Da farko dai ina yin la’akari da irin kasar jihar Jigawa. Kasar da mutum ke yin noma a cikin ta ce ma’aunin hankalin abin da mai noma zai shuka. Domin akwai abin da ko ka kawo ka noma a wata kasar, ba zai yi ba.

Na biyu kuma ni a kasuwa kawai na ke zuwa sayi irin da zan noma. Ba na jira, domin idan ka yi jinkiri, sai irin ya kare ba ka kai ga saye ba.

PT: Ba ki taba jin labarin irin zamani na gwamnati mai samar da yabanya ba ne?

Sabuwa: Ina jin labarin sa, tabbas. Na kan same shi a Hukumar Raya Harkokin Noma ta Jihar Jigawa, wato JASCO.

PT: Ko ki na amfani da injinan noma na zamani

Sabuwa: Ba ni da karfin saye ko aro ko daukowa haya in dai ana maganar kayan noma na zamani ne. Majiya karfi na ke samu ’yan ga-noma su yi min noma ko wani aikin gona na biya su.

PT: To yaran ki da ki ka haifa su uku fa? Ko sun kai karfin taiamaka maki a gona?

Sabuwa: Kwarai su na yi min aiki a gona, amma biyan su na ke yi, kamar yadda na ke biyan sauran ma’aikata.

PT: Kamar buhunna nawa na amfanin gona ni ke nomawa a shekara?

Sabuwa: To cikin 2019 dai na samu buhun shinkafa 30. Amma cikin 2020 na dibga asara, saboda ruwan sama.

Duk da haka na samu dawa buhu 20 haka gyara buhu 20, kowane mai nauyin kilogiram 50.”

Sabuwa ta ci gaba da bayyana cewa ta kan tanadi buhunna wadanda ta ke adana kayan amfanin gonar ta.

Sannan kuma ta ce ta na ci a gida, amma wanda ta ke sayarwa ya fi yawa.

Ta ce babu wasu dillalan da ta ke bai wa amfanin gonar ta su kai kasuwa su sayar mata. Ta ce ita da kan ta ke daukar kayan gonar ta ta kai kasuwa ta sayar.

PT: To yanzu ta yaya ki ke samun takin zaman kuwa?

Sabuwa: Mu dai a nan takin zamani ya na matukar wahala sosai. Ba na amfani da takin zamani kuma saboda tsadar da ya ke da shi a nan inda na ke.

Ta ce idan damina ta sauka, gyada ta ke fara nomawa kuma a lokacin ta na da wadataccen lokacin da za ta maida hankali ga kiwo.

Sabuwa ta ce ba ta taba amfana da wani tallafi ko lamuni koramce daga gwamnati ba.

Ta ce ta kashe kudade za su kai naira 200,000 ga kowace hekta daya. Wato ta kan kashe naira 400,000 kenan a hekta biyu da ta ke nomawa.

Da aka tambaye ta batun riba, Sabuwa ta kara da cewa farashin buhun shinkafa naira 17,500. Dawa kuma naira 16,000, sai masara naira 16,000. Da na sayar da amfanin gona na naira 875, ribar naira 345,

Amma a hekta biyun da na noma, na samu ribar naira 585,000.

Sabuwa ta ce a kasuwar Gujungu ta ke kai kayan gonar ta ta sayar.

Batun kungiya kuwa, cewa ta yi ta na cikin Kungiyar Kananan Manoma Mata wato SWOFAN.

Share.

game da Author