• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    GANAWAR TINUBU DA NLC: Ƙungiyar Ƙwadago ta ce a tilas a soke ƙarin kuɗin mai, an shammaci ‘yan Najeriya

    Buhari-signing-2020-budget

    Gwamnatin tsohon shugaban kasa Buhari ta sanar da sabbin nade-nade a daidai ana rantsar da Tinubu shugaban kasa

    Minista Sadiya ta miƙa ragamar Ma’aikatar Harkokin Jinƙai ga Babban Sakatare

    2015-2023: ‘Na yi sukuwa ta lafiya, na kai zamiya lafiya’ – Buhari

    BANKWANA DA BUHARI: ‘Tinubu yau mafarkin ka ya zama gaskiya, Allah ya sa ka kai Najeriya fiye da inda na kai ta’ – Nasihar Buhari ga Asiwaju

    Tsakanin Sanata Barau da Gwamna Ganduje, Daga Jaafar Jaafar

    Ba zan jira Litinin ba, tun Lahadi zan mika mulki ga Abba Gida-Gida in kama gaba na – Ganduje

    RANTSAR DA TINUBU: Kotun Koli ta yi watsi da karar rashin cancantar Tinubu shiga zaɓen 2023

    RANAR RANTSAR DA TINUBU: Za mu hana makiyaya karakaina da shanu a cikin Abuja – Shugaban Miyetti Allah

    An Karrama gidan Jaridar PREMIUM TIMES da kyauta mafi daukaka a aikin Jarida na kasar Amurka

    BA DA MU BA, TAYA ƁERA ƁARI: PREMIUM TIMES ta nesanta kan ta daga ƙungiyar da ta jona sunan ta a shirya taron karrama wasu mutane

    KIRAN RUWA: ‘Ka wa Allah ka ɗaga mana kafa, kada ka kwace mana filayen mu har 9 da ka kunno kai a kan su – Makarfi ga El-Rufai

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

    QATAR 2022: 2:1: Saudiyya ta kafa tarihin karya gadara da tutiyar buga wasan Agentina 36 a jere babu rashin nasara

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    BIDIYO: NAJERIYA @62: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da mulkin Buhari a tsawon shekaru 7 da suka gabata

    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

No Result
View All Result

Gwamnonin Najeriya sun yi tir da Gwamnan Kogi, kan tozarta allurar korona da ya yi

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
January 22, 2021
in Manyan Labarai
0
Gwamnonin Najeriya sun yi tir da Gwamnan Kogi, kan tozarta allurar korona da ya yi

Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta yi Allah-wadai da kalaman da Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya yi, inda ya ce allurar korona ta na kisa, don haka duk wanda ya sake aka yi masa, to ya kuka da kan sa.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin na NGF, Fayemi Kayode na Jihar Ekiti ne ya yi tir da Yahaya Bello a ranar Juma’a, bayan tashin gwamnonin daga taron su na farko na shekarar 2021.

Sai dai an yi taron ta nesa-nesa, wato kowane gwamna daga ofishin sa.

“Gwamnoni mun zauna mun tattauna batun yadda za a samar wa jama’a allurar rigakafin korona da kuma yadda za a yi wa jama’a allurar.

“Sai dai kuma kasassabar da daya daga cikin mu ya yi kan allurar korona, inda har aka buga manyan jaridun kasar nan, mu na sanar da jama’a cewa mun barranta daga kalaman da ya yi. Shi ya yi kidan sa, kuma shi kadai ya yi rawar sa.

“Kungiyar Gwamnonin Najeriya na sanar da cewa za su ci gaba da bin turbar abin da kimiyya ya samar da kuma ya nuna ya kamata a yi amfani da shi.

“Kuma za mu tabbatar mu na bin duk abin da aka zartas daga bangaren kwararru, wanda duk mu ka tabbatar zai amfani jama’a, ba tare da mun yi karambanin cusa wani murdadden ra’ayin mu ba.

Sannan kuma Fayemi ya yi wa sauran gwamnoni bayanin sakamakon ganawar da ya yi tare da Shugaban Hukumar Gudanarwar Global Allience for Vaccine Innunization (GAVI).

Ya ce allurar rigakafin korona ba abin tsoro ba ce, domin duk duniya yanzu ita ake rububi, a matsayin maganin dakile annobar korona.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin da Gwamna Yahaya Bello ya ce duk wanda aka dankara wa allurar korona bingirewa zai yi ya mutu.

Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi, wanda ya rika zabga karairayin cewa babu cutar korona a jihar Kogi, yanzu kuma ya bijiro da sabon kamfen, na tinzira jama’a kada su yarda a dankara masu allurar rigakafin cutar korona.

Bello ya fara wannan kamfen a daidai lokacin da duniya baki daya ta maida hankali wajen kirkirowa, samarwa, saye da mallakar rigakafin korona, shi kuma ya maida hankali wajen karyata cutar tare da hana mutane yarda a yi masu rigakafin ta.

Wannan lamari ya za daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta na zaman jiran kwalaben allurar rigakafin korona daga kamfanin Pfizer da BioNTech nan da karshen watan Janairu.

Sai dai kuma masana harkokin lafiya da kungiyoyin da su ka jibinci lafiya da magunguna na duniya sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa, “ba fa zai taba yiwuwa Najeriya ta samu allurar rigakafin korona nan da karshen Janairu ba.’’

Jami’an gwamnati a Fadar Shugaban Kasa sun bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakin sa Yemi Osinbajo ne za a fara yi wa allurar rigakafin korona a kasar nan.

Sun ce kuma kai tsaye za a nuno su a lokacin da ake yi masu allurar a talbijin kowa ya gani.

Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti, ya gana da Shugaba Buhari, inda bayan ganawar da suka yi ya shaida wa manema labarai cewa su ma gwamnoni a fili za a yi masu allurar kai-tsaye za a nuno a gidajen talbijin.

“Kada fa ku manta, mu na da sani da fahimta a kan batun rigakafin nan. Mun yi kokari mun dakile cutar foliyo ta hanyar rigakafi.” Haka Fayemi ya ce, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya.

Duk Wanda Korona Ba Ta Kashe Ba, To Allurar Rigakafin Korona Za Ta Kashe Shi -Yahaya Bello:

An nuno Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi a cikin wani bidiyo ya na ingiza mutane kada su sake su yarda a yi masu allurar rigakafin korona.

Bidiyon dai tun a ranar Lahadi aka fara watsa shi a soshiyal miiya, musamman a shafukan Facebook.

“..Su na so su yi amfani da rigakafin korona su kashe ku, su kashe mu. Allah ya kiyaye! Wa zai yarda a yi masa allurar korona!” Inji Yahaya Bello.

Bello dai na ci gaba da kushe allurar rigakafin korona, wadda a yanzu kasashe kusan 50 a duniya ke ta tseren samarwa a kuma mallaka.

“Wai ana cewa an samo rigakafin cutar korona a cikin shekara daya da bayyanar cutar. Alhali kuma har yau an kasa samun rigakafin cutar kanjamau, zazzabin maleriya, sankara da wasu cututtuka masu yawa da ke kashe mutane.

“Duk mai hankali ya waiwaya baya, ya tuna abinda ya faru a Kano, lokacin da aka gurgunta kananan yara masu yawa, wadanda aka yi wa allurar gwajin rigakafin foliyo.

“Mu dai mun dauki darasi. Ba za a yi mana rigakafin korona ba.”

“Idan sun ce za su ta su allurar a gaban idon jama’a, ku rabu da su, can su je su karata. Kada ku ce na ce kada a yi maku rigakafi. Amma duk wanda ya ga zai iya kai kan sa a dankara masa allurar rigakafi, to ya bude idon sa tangaram, kafin ya saida ran sa a yin masa allurar.” Inji Yahaya Bello.

Idan ba a manta ba, Yahaya Bello ya sha karyata cutar korona. Har hanawa ya yi a rika yin gwaji a jihar sa.

Akwai ma lokacin da ya fatattaki jami’an Hukumar NCDC daga jihar, wadanda ya ce idan ya bude ido ya gan su a gaban sa, zai sa a kulle su a killace su tsawon makonni uku. Ya ce ba zai yarda su kai korona jihar Kogi daga Abuja ba.

Bello wanda shi ne gwamna mafi karancin shekaru, ana rade-radin ya na son fitowa takarar shugaban kasa a karkashin APC, kamar yadda kakakin jihar Kogi ya fara yi masa kamfen.

Tags: AbujaFayemiHausaNajeriyaPREMIUM TIMESYahaya Bello
Previous Post

Sauya fasalin Najeriya kadai ba zai magance matsalolin mu ba – Jonathan

Next Post

Kashi 17% ne na ƴan Najeriya har yanzu ke shakkun Korona – Bincike

Ashafa Murnai

Ashafa Murnai

Next Post
Mutum 9 cikin 10 a jihohin Sokoto, Taraba da Jigawa fakirai ne tuburan – Rahoton NBS

Kashi 17% ne na ƴan Najeriya har yanzu ke shakkun Korona - Bincike

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • SHARI’AR ZAƁEN SHUGABAN ƘASA: Tinubu da INEC sun ƙi amincewa da tulin kwafe takardun da Atiku ya kwafo daga iReV
  • GANAWAR TINUBU DA NLC: Ƙungiyar Ƙwadago ta ce a tilas a soke ƙarin kuɗin mai, an shammaci ‘yan Najeriya
  • HAJJI 2023: Gwamnatin Filato ta bar mahajjatan jihar su na hajijiya a Madina
  • Kada ku tausaya min don na faɗi zaɓen Sanatan Zamfara – Sanata Marafa
  • JIRAN TSAMMANI: Tinubu zai saka wa waɗanda su ka yi wa APC hidima da waɗanda su ka wahala saboda jam’iyya – Marafa

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.