Gwamnatin Tarayya ta rattaba hannu kan Yarjejeniyar Habbaka Nau’in Kayan Gona da Abinci

0

A ranar Laraba ce Gwamnatin Tarayya ta rattaba hannu a kan tsohuwar yarjejeniyar Inganta Kayan Gona da Bunkasa Kayan Abinci ta hanyar dabarun inganta noma ta ‘Genetic Resources for Food and Agriculture.

Ministan Harkokin Noma da Raya Karkara, Sabo Nanono ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa.

Ya yi wannan zantarwar bayan fitowa daga Taron Majalisar Zartaswa na farko a shekarar 2020.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya jagoranci taron.

Sai dai kuma baya ga shi da Mataimakin sa, Yemi Osinbajo da Sakataren Gwamnatin Tarayya da kuma Shugabar Ma’aikata, Ministocin da su ka halarci taron ba su da yawa. Sauran duk daga ofishin su su ka halarci taron, wato abinda ake kira ‘virtual’.

Nanono ya ce an rattaba wa yarjejeniyar hannu domin a kara bunkasa harkokin noma ta hanyar bincike da kuma kara yawan kayan abincin da ake nomawa a cikin gida.

“Amfanin rattaba hannu a kan wannan yarjejeniya dai domin a kara yawan kayan abinci da inganta harkokin noma, ta hanyar amfani da yawan mambobin kasashen da ke cikin kungiyar.” Inji Nanono.

Ya ce Najeriya ta dade da sa hannu kan yarjejeniyar, amma sai a ranar Laraba din ce Majalisar Zartaswa ta rattaba hannu a kan yarjejeniyar.

Daga nan sai Nanono ya ce daga yau Najeriya ta zama cikakkar mamba din kasashen da ke cikin wannan yarjejeniya, wadanda sun haura 160.

“A takaice dai wannan yarjejeniya an kulla ta ne domin kasashen da ke cikin ta su bunkasa harkokin noma. Kuma yarjejeniyar ta kunshi kasashe 167.”

Tun cikin watan Nuwamba, 2001 aka zartas da yarjejeniyar a Taron Hukumar Kula da Abinci ta MajalisarDinkin Duniya (FAO).

Makasudin yarjejeniyar dai shi ne a bijiro da dabarun bunkasa kayan abincin da ake shukawa bisa yin mafani da kimiyya tare da yin raba daidai din dabaru da kuma fa’idojin a aka samar wajen bunkasawar.

An fara aiki da yarjejeniyar tun cikin 2004, da nufin samarwa da amicewa gudummawa ga manoma somin fadada dabarun noma, masu bunkasa kayan abinci a duniya baki daya.

Ya zuwa cikin watan Fabrairu, 2020, akwai kasashe 147 da kuma kuniya daya a matsayin mambobin kasashen da ke cikin yarjejeniyar.

Da ta ke magana, Daraktar OFAB ta Afrika da Najeriya, Rose Gidado, ta ce wannan jarjejeniya ta zo daidai da lokacin da aka fi bukatar dabarun samar da wadataccen abinci a duniya baki daya.

“Saboda sai an samu wadataccen abincin da za a ci, sannan za a fara batun neman lafiya.”

Share.

game da Author