Mataimakin gwamnan jihar Kano Nasiru Gawuna ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta horas da manoma 20,000 a jihar.
Gawuna ya ce gwamnati ta horas da manoman ne ta hanyar shirin ta na APPEALS da gwamnati ta kirkiro a shekaran 2016.
Ya ce gwamnati ta tsaro wannan shiri ne domin inganta aiyukkan noma ta hanyar wayar koyar da su sabbin da dabarun noman zamani, samar da aiki da abinci domin inganta tattalin arzikin kasa.
Gawuna ya ce gwamnati za ta horas da manoman shinkafa, alkama da tumatir sama da 10,000 dabarun noma na zamani da kasuwanci.
Ya ce daga cikin wannan yawa shirin ya horar da manoma 6,344 sannan shirin ya kuma horar da mata, matasa da masu fama da nakasa a jikinsu 1,700 kiwon kifi da kaji.
Gawuna ya ce bayan an kammala horas da manoma gwamnati za ta basu kudaden jari da kayan aiki domin su fara sana’a.
Manajan shirye-shirye na APPEALS Dr Salisu Garba ya ce gwamnati ta kirkiro wannan shiri ne tare da hadin gwiwar babban bankin duniya.
Garba ya ce tun bayan kirkiro Shirin a shekarar 2016 ake gudanar da irin wannan horaswa a wasu jihohin kasar nan.
PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda Gwamnatin jihar Kano ta raba injinan banruwa 5,000 wa manoma domin inganta aiyukan noman rani a jihar.
Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Murtala Sule-Garo ya ce gwamnati ta tura ma’aikatan noma don taimakawa manoma da koyar dasu dabarun aikin gona na zamani a duk kananan hukumomi 44 dake jihar.
Discussion about this post