Gwamnatin jihar Kebbi za ta siyar wa talakawa 22,000 filaye su gidajen kansu a farashi mai sauki a jihar.
Kwamishinan filaye da gidaje na jihar Abubakar Sadiq ya sanar da haka a fadar gwamnati a garin Birnin Kebbi ranar Laraba.
Sadiq ya ce gwamnati ta yi haka ne domin talakawa su mallaki gidajen kansu sannan da kawar da matsalolin rashin gidajen zama ga mutane da jihar ke fama da shi.
Sadiq ya ce gwamnati za ta raba filaye 7,000 a Birnin Kebbi 1,500 a Argungu, Yauri da Zuru sannan 535 a sauran kananan hukumomin jihar.
Ya yi kira ga masu bukatar filayen da su garzaya ofishin ma’aikatar fili dake jihar domin siyan fom din filin.
Sadiq ya ce an raba filayen zuwa wuraren da ake da yawa, wuraren da babu yawa sosai da wuraren da suke da matsakaicin yawa.
A Birnin Kebbi a wuraren da ake da yawa za a siyar da filayen a kan Naira 200,000, Naira 150,000 a wuraren dake da matsakaicin yawa sannan 100,000 a wuraren da basu da yawa sosai.
A Kananan hukumomin Argungu, Yauri da Zuru gwamnati za ta siyar da fili akan Naira 100,000 a wuraren da ake da yawa, Naira 150,000 a wuraren dake da matsakaicin yawa sannan Naira 120,000 a wuraren da basu da yawa sosai.
Bayan haka kwamishinan kananan hukumomi da sarakunan gargajiya Hassan Mohammed-Sallah ya ce za a ci gaba wannan shiri domin tallafawa tallakawa a jihar.
Shugaban kungiyar ciyamomin kananan hukumomi na jihar ALGON), Shehu Sarkin-Kabi-Jega ya yi kira ga mutane da su gaggauta siyan fom din domin ganin sun mallaki gidajen kansu a jihar.