Gwamnatin Buhari za ta fara sayar da kadarorin gwamnati domin a samar wa kasafin 2021 kudi

0

Baya ga shirin ramto kudade a kasashen waje da kuma nan cikin gida, Gwamnatin Tarayya za ta saka wasu kadarorin gwamnati a kasuwa, domin a sayar a samu kudaden zubawa cikin kasafin 2021.

Ministar Harkokin Kudade Zainab Ahmed, ta tabbatar da shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ke yi domin fara sayar da wasu kadarorin gwamnati da niyyar samun kudaden da za a yi ayyukan kasafin 2021 da su.

Wannan tunanin sayar da kadarorin ya na cikin wani kundin daftari da gwamnatin tarayya ta damka wa Majalisar Tarayya.

Sannan kuma gwamnatin ta ce za a sayar da wasu kadarorin da ban a harkokin mai ba duk dai a zuba kudaden cikin kasafin na 2021.

Bayanan su na cikin wani daftarin da Ministar Kudade Zainab Ahmed ta damka wa Majalisa a ranar Talata.

Kuma tuni wadannan takardun bayanai sun fado hannun PREMIUM TIMES.

Bayanan dai gwamnatin tarayya ta sa masu hannu ne a ranar 12 Ga Janairu, 2021.

Tun a ranar 23 Ga Disamba ne dai aka sa wa Kasafin Kudi Hannu, inda aka amince za a kashe naira tiriliyan 13.58.

Sai dai kuma daga cikin kudaden, naira tiriliyan 5.02 duk bashi za a ciwo.

Sannan kuma za a kashe naira tiriliyan 3.3 wajen biyan basussukan da ake bin Najeriya daga cikin kasafin na naira tiriliyan 13.58 din.

Sai kuma naira tiriliyan 5.6 da za a kashe wajen biyan albashin ma’aikata.

Sai naira tiriliyan 4.1 da za a kashe wajen yin manyan ayyuka a cikin kasa.

Hakan ya nuna za a samu gibin naira tirilliyan 5.2 (5,196,007,992,292) kenan, wadanda su ne za a shiga duniya a ciwo bashin su.

Jama’a da dama dai nuna rashin amincewa a ciwo wannan dimbin bashi. Ga shi kuma idan an hada da bashin cikin gida, kudin da gwamnatin Buhari za ta ciwo bashi zai kai naira tiriiyan 5.6 kenan.

Sai dai kuma gwamnati ba ta bayyana sunayen kamfanoni ko kadarorin da za ta sayar ba. Sannan kuma ba ta bayyana ko naira nawa ta ke nema wajen sayar da kamfanonin ko kadarorin ba.

Amma kuma cikin watan Nuwamba, 2020 dai Kwamitin Lura da Saida Kadarorin Gwamnati ya cika da mamakin yadda aka shigo da batun sayar da hannayen jarin gwamnati da kadarorin ta, ba tare da sanin Majalisa ba.

Sai da aka zo wajen bayanan kare kasafin kudin 2021 ne batun sayar da kadarori da hannayen jarin ya bulla.

Kadan Daga Kadarorin Da Za A Sayar:

Tashar Makamashi ta Geregu

Tashar Makamashi ta Otomosho

Tashar Makamashi ta Calabar

Dukkan su za a yi masu kudin goro, a sayar da su kan farashi naira bilyan 434 a cikin 2021.

Za A Bayar Da Aron:

National Arts Theatre

Tafawa Balewa Square

River Basin Development Authority

Dukkan su a kan kudi naira milyan 836 lada.

Sai kuma Babban Sitadiyan Na Kasa da ke Abuja da wasu kamfanonin su kuma a kan kudi naira milyan 100.

Sai dai kuma Shugaban Kwamitin Sayar da Kadarorin Gwamnatin na Majalisar Dattawa, Sanata Theodore Orji, ya ce ba su san da zancen ba.

Sannan kuma ya ce Daraktan Sayar Da Hannayen Jari na Kasa (BPE), Alex Okoh bai sa su cikin harkar sayar da kamfanonin ba.

Sai dai kuma Magatakardar Kwamitin Sayar da Hannayen Jarin, Sadia Abdullahi, ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa yanzu an sasanta, an fahimci juna. Kuma sun gyaro ta a tsakanin su.

Share.

game da Author