Wani sakamakon binciken da manyan gwamnatin Najeriya su ka bibiya, ya fallasa yadda ake samun yawaitar rashawa, ragabza, bushasha, rashin iya aiki a hukumomin gwamnatin tarayya da dama.
Wani jami’i ne ya tabbatar da haka a sanarwar da aka fitar ranar Laraba.
Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne da kan sa ya gabatar wa Majalisar Tattalin Arziki wannan rahoton a ranar Laraba, kamar yadda Kakakin Yada Labaran sa, Laolu Akande ya fitar a cikin wata sanarwa.
Rahoton dai wata kungiya ce mai suna PwC ta gudanar da binciken.
“A taron Majalisar Tattalin Arzikin Kasa wadda Matamakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya shugabanta a ranar Laraba, an amince za a mika sakamakon wannan rahoton bincike ga dukkan hukumomin da abin ya shafa, domin nuna masu lallai gwamnati fa ta damu da irin abin da PwC ta bankado.” Inji Akande.
Ya ce za a gabatar wa wadannan hukumomi da cibiyoyin gwamnati wannan rahoto domin kokarin tabbatar da gyara da kuma tsabtace hukumomin.
Ya ce Kwamitin Samar da Hanyoyin Gudanar da Harkokin Kasuwanci a Najeriya (PEBEC) sun yanke shawarar gabatar wa hukumomin sakamakon binciken da PwC su ka bankado, wanda ya fallasa matsaloli da irin rashawa da bushashar a ake yi a hukumomin.
Shi dai wannan sakamakon binciken, ya ta’allaka ne kan bankado yadda hukumomin ke aiki a kan ka’ida ko kuma rashin yin aiki a kan ka’da.
Sakamakon na sa kuwa ya tabbatar da fallasa yadda ake samun yawaitar rashawa, ragabza, bushasha, rashin iya aiki da dafkal a hukumomin gwamnatin tarayya da dama.
Sai dai kuma Osinbajo ya ce a rahoton an nuna wadansu kurakuran da ake samu a wasu hukumomin da abin ya shafa, ba da gangan ba ne.
Ya ce ana samun kurakuran saboda mutum tara ya ke, bai cika goma ba.
“Inda ake samun mai dokar barci na bingirewa da gyangyadi, to babu yadda za a a samu yanayin kirki da har kasuwanci zai yi tasiri a kasar nan. Idan aka zuba ido kuwa, tamkar mu na kirari ne mu na burma wa cikin mu wuka.” Inji Osinbajo.
“Na amince duk mai laifi a wannan lamari, idan shugaban wata hukuma ne, to a dora masa laifin sa kawai. Shi ma idan ma’aikatan da ke karkashin sa ne ke da laifin, sai ya dora masu.
“Amma idan aka rika tafiya a haka ba tare da an dauki matakin komai ba, to fa akwai matsala gagarima.”
Wasu da suka halarci taron sun hada da Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Otumba Niyi Adebayo, wanda shi ne Mataimakin PEBEC, sai Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed, Ministan Sufuri Rotimi Amaechi da Ministan Harkokin Yada Labarai, Lai Mohammed.
Akwai Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, Karamin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Clem Abga da waikilai daga Majalisar Dattawa da ta Tarayya da kuma wakilan PwC, kungiyar da ta gudanar da binciken.
Discussion about this post