Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana cewa gobara ta yi sanadiyyar rayukan mutum 134 da dukiyar mutane da ya kai naira miliyan 635 daga watan Janairu zuwa Disambar 2020 a jihar.
Jami’in yada labarai na hukumar Saidu Muhammad ya sanar da haka da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Kano ranar Talata.
Saidu ya ce hukumar ta ceto rayukan mutum 1,077 da kaya da ya kai Naira biliyan 2.56 a gobara 786 da aka yi a cikin shekarar 2020.
“Rashin mai da hankali a lokacin da ake girki da kuma rishon girki mai amfani da iskar gas sannan da amfani da kayan wutan lantarki duk sune suka sa aka rika samun yawa-yawan gobara a kasar.
Saidu ya ce an kira lambar hukumar domin ta kawo dauki sau 693 amma kuma daga ciki 184 karya ne, ” wasu ne kawai ke kiran mu ‘yan dadi waya, sai munzo muga ashe karya ne”.
Saidu ya yi kira ga iyaye da su daina bari kananan yara wasa kusa da rijiyoyi da wuraren dake da hadari.
Discussion about this post