Hukumar kula da ingancin magani da abinci na ƙasa NAFDAC ta yi kira ga mutane da su yi hattara domin jabun maganin Korona ya darkako.
Shugaban hukumar Mojisola Adeyeye ta yi wannan gargadi ranar Juma’a.
“Har hanzu hukumar NAFDAC ba ta samu sumfurin maganin rigakafin da ak ikirarin an hada ba kuma idan kamfanin dake hada maganin da gaske yake yi ya kawo samfurin maganin rigakafin da yake hadawa domin hukumar ta tabbatar da ingancinsa.
“Muna kira da yin gargadi ga ‘yan kasuwa kada su fada tarkon wadannan kamfanoni, su fara shigowa da maganin.
Idan ba a manta ba, kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar Korona, ya ce da zaran maganin rigakafin ya iso Najeriya, za a yi wa Buhari da mataimakin sa a talbijin kowa ya gani.
Haka kuma suma gwamnoni, sun yi irin wannan kuri inda suka idan maganin ya iso Najeriya, za su yi allurar a talbijin kowa a jihohin su ya gani.
Hakan wai shine zai tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa maganin da gaske ne kuma kmowa ya yarda ayi masa.
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1867 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Juma’a.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –713, Filato-273, FCT-199, Kaduna-117, Oyo-79, Enugu-58 Ondo-53, Kano-49, Sokoto-43, Ogun-37, Osun-37, Nasarawa-36, Rivers-28, Benue-24, Delta-24, Niger-24, Gombe-18,Edo-15, Taraba-12, Bayelsa-10, Ekiti-9, Borno-6, Zamfara-2 da Jigawa-1.
Yanzu mutum 107,345 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 84,535 sun warke, 1,413 sun rasu.
A ranar Alhamis , mutum 1479 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Filato, Nasarawa, Rivers, Edo da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.