GARGADIN BUHARI: Ku kiyaye dokokin Korona gudun kada a sake garkame Kasa – Fadar Shugaban Kasa

0

Kakakin fadar shugaban Kasa Garba Shehu ya gargadi ‘yan Najeriya su tsananta kiyaye bin dokokin Korona idan ba haka ba gwamnati za ta sake saka dokar hana walwala kowa ya zauna a gida na wani lokaci kuma.

“Gwamnatin Buhari ba ta da son kulle kasar nan shune ya sa ta ke ta yin kira ga ‘yan akasa da su tsananta kiyaye bin dokokin Korona a da aka gindaya domin gujewa hakan.

” ‘Yan Najeriya ba za su so ace an sake saka dokar Kulle a kasar nan ba, saboda mafi yawan su sai sun fita ne suke iya samar wa iyali abincin da za su ci a rana. Kuma samar wa mutane tsaro da kariya ga rayuka da lafiyar su shine aikin duk gwamnatin da ke son kawo wa wa mutanen ta ci gaba.

Tunda aka shiga sabuwar shekarar 2021 Korona ta tsananta a Najeriya fiye da shekarar baya a lokacin da cutar ta bullo a duniya.

Haka kuma mutuwa daga cutar ya karu matuka inda a jere a kwanakin nan sai an samu wadanda suka rasu a dalilin kamuwa da cutar.

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1,883 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Asabar.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum –1040, FCT-298, Anambra-86, Rivers-54, Taraba-45, Ogun-42, Oyo-40, Akwa Ibom-38, Sokoto-30, Ebonyi-30, Imo-28, Kaduna-28, Osun-27, Kano-21, Benue-19, Edo-17, Gombe-15, Ekiti-9, Delta-8, Jigawa-3, Kwara-2, Bayelsa-2 da Filato-1.

Yanzu mutum 130,557 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 103,712 sun warke, 1,578 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 25,267 ke dauke da cutar a Najeriya.

Share.

game da Author