Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa har yanzu dokar hana shigo da shinkafa daga kasashen waje ta na nan daram.
Kwanturola na Kwastan mai lura da Sokoto da Zamfara, Abdulhamid Ma’aji ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke sake bude kan iyakar Illela zuwa cikin Jamhuriyar Nijar a jihar Sokoto.
Manyan jami’an gwamnatin Najeriya da na Jamhuriyar Nijar ne su ka halarci kwarya-kwaryar bikin sake bude kan iyakar.
Daga nan sai Ma’aji ya ce za a ci gaba da rika sa-ido domin tabbatar da an tsaftace kan iyakar daga shigowa da kayan fasa-kwaurin da aka haramta shigowa cikin Najeriya da su.
Ya nuna takaicin yadda ake shiga da dimbin kayayyakin da Najeriya ta haramta, ta hanyar bi da su ta hanyoyin kasa.
Shugaban Kungiyar Masu Fiton Kaya, wato ‘’yan kiliyarin’, Aminu Dan’iya, ya bayyana cewa akwai kamfanonin fiton kayayyaki har 34 da su ka yi rajista a kan iyakar Illela.
Ya ce dukkan su za su rika bin ka’idojin da gwamnatin Najeriya ta shimfida.
Wannan gargadi kan buhunan shinkafa da gwamnati ta yi, ya zo ne kwana daya bayan da PREMIUM TIMES HAUSA ta buga wani furuci da Ministan Harkokin Yada Labarai, Lai Mohammed yay i, cewa an kwace buhunan shinkafa 157,511 cikin wata biyar.
Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ya gamayyar jami’an tsaro sun kwace buhunan shinkafa 157,511, wadanda duk manyan buhuna ne masu nauyin kilogiram 50.
Ya ce an kwace su daga hannun masu fasa-kwauri tsakanin Agusta da Oktoba lokacin da aka shigo da su kasar nan ta barauniyar hanyoyi bayan an kulle kan iyakokin kasa.
Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ne ya bayyana haka a Lagos ranar Litinin, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa an kama bakin-haure har 1,375 a tsawon lokacin da kan iyakokin Najeriya su ka kasance a kulle.
An kama bakin-hauren a tsakanin watan Agusta 2019 zuwa 17 Ga Disamba 2020.
Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ne ya bayyana haka a Lagos ranar Litinin, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai.
Ministan ya kara da cewa an kwace buhunan shinkafa 157,511, wadanda duk manyan buhuna ne masu nauyin kilogiram 50.
An kuma kwace buhunan takin zamani 10,447 samfurin NPL da ministan y ace ana amfani da su ne ana hada bom na gargajiya.
An kuma kwace jarka 18,630 ta man girki.
Lai ya kiyasta kudaden kayan da aka kama za su kai naira bilyan 12.362.
Ya ce an kama kayan bayan an kaddamar da shirin tsare kan iyakokin Najeriya a dukkan yankunan ksar nan.
Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Tsaro ya shirya atisayen domin bunkasa tattalin arziki da kuma tsare kan iyakokin Najeriya.
Shirin ya kunshi gamayyar jami’an kwastan, jami’an shige-da-fice, sojojin Najeriya da jami’an ’yan sanda da sauran jami’an leken asiri.
An dai bude kan iyakokin Najeriya a ranar 16 Ga Disamba bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarni.
Kan iyakokin da aka bude sun hada da Seme, Illela, Maigatari da Mfun.
Ya ce an samu nasarar dakile shigo da muggan makamai, muggan kwayoyi da sauran haramtattun kayan da Najeriya ta hana yin fasa-kwaurin su.
Sannan kuma ya ce an samau nasarar bunkasa tattalin arziki da kuma inganta tsaro da bunkasa harkokin noma a cikin kasar nan.
Discussion about this post