Ganduje zai kafa Askarawan Korona a Jihar Kano

0

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya bayyanawa manema Labaria a garin Cewa gwamnati za ta kafa kungiyar duba garin Korona a jihar Kano.

Gwamna Ganduje ya ce gwamnati ta yi haka ne domin a tilasta wa mutane bi da kiyaye dokokin korona a fadin jihar.

” Dole mu maida hankali matuka wajen kawo karshen yaduwar cutar Korona a jihar Kano. Ba za mu sa ido mu bari ta cigaba da fantsama a tsakanin mutanen mu ba.

Ganduje ya ce za a kafa wannan kungiya ta hadin gambiza ce, wanda zai hada da jami’an ‘yan sanda, Sibul Difens da wasu da za a dauka domin tabbatar an yi nasara a wannan aiki.

A karshe Ganduje godewa masu makarantu masu zaman kansu kan yadda suke kokarin taimakawa gwamnati wajen kiyaye dokar Korona.

Share.

game da Author