Ganduje ya ziyarci Iyalan Kwankwaso domin yin Ta’aziyyar rasuwar mahaifin tsohon gwamnan

0

Gwamnan Kano ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi makaman Karaye Musa Saleh Kwankwaso, wato mahaifin tsohon gwaman jihar Rabiu Musa Kwankwaso.

Sai dai kuma ko da ya kai ziyarar ta’aziyyar ba su hadu da Kwankwaso a wajen ta’aziyyar ba.

Kanin tsohon gwaman Kwankwaso, Baba musa Kwankwaso ya amshi bakuncin gwamna Ganduje a garin Madubi.

Ganduje ya ve baya kasar ne a lokacin da mahaifin Kwankwaso ya rasu.

A cikin jawabin da Ganduje yayi ya shaida cewa gwamnati za ta bar sarautar Hakincin sarautar Kwankwaso a gidan Musa Sale Kwankwaso.

” Marigayi Musa Saleh, mutum ne mai mutunci da sanin yakamata sannan mai hakurin gaske. Za mu ci gaba da girmama gidan nan kuma ba za a taba sarautar da gidan ya gada.

Iyalan marigayi Musa Saleh sun gode wa gwamna Ganduje bisa wannan karamci da yayi wa gidan.

Share.

game da Author