Gwamnatin Jihar Ondo ta maida wa Fadar Shugaba Muhammadu Buhari raddi, dangane da yadda fadar ta yi kakkausan suka ga jihar Ondo, don ta bada wa’adin kwanaki bakwai ga Fulani makiyaya da ke cikin dazukan-gwamnatin jihar cewa su fice daga ciki.
Kamishinan Yada Labarai na Jihar Ondo, Donald Ojogo, ya bayyana cewa martanin da Kakakin Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ya yi a Ondo, ya fi kama da cea fadar ta fi nuna tausayi ga Fulani makiyaya fiye da ko a kasar nan.
“Furucin Garba Shehu ya nuna inda fadar gamnatin tarayya ta fi nuna tausayi. Hakan dai babbar barazana ce ga dorewar zamantakewar jama’ar kasar nan a wuri daya.” Inji Ogoja.
“Mu na neman karin bayani daga gamnatin tarayya a yi mana dalla-dalla shin ko rashin mutuncin da masu fakewa da kiwo ke yi su na garkuwa da mutane, ko sun dogara ne da jingina ga bangon masu mulkin da su ke takama ne? Gaskiya ana yi a hakin kankasar nan barazana.”
Tankiyar ta samo asali tun daga ranar Litinin, bayan Gwamna Rotimi Akeredolu ya haramta wa makiyaya kiwo a cikin dajin-gwamnatin jihar Ondo.
A martanin Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ya bai kamata a tauye wa makiyayan hakkin su na kiwo ba. Kamata ya yi a zauna a sasanta, a fitar da baragurbi daga cikin su.
Gwamnatin Jihar Ondo ta maida martani kamar haka:
“Abin tambaya a nan, shin wai wadannan makiyaya masu kashe mutane su na garkuwa su na fashi da makami, sun fi sauran jama’a da ita kan ta Gwamnatin Tarayya muhimmanci ne?
“Kuskure ne mutum ya fake cikin fadar shugaban kasa ya na fitar da maitar sa ta kabilanci a fili.”
PREMIUM TIMES ta tuntubi Ogoja a ranar Laraba inda ya tabbatar mata cewa ya yi wannan bayani.
Sannan kuma ya ce wa’adin da aka ba makiyayan na nan, ba za a fasa fatattakar su ba.
PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin yadda Gwamnatin Ondo ta fatattaki Fulani makiyaya daga dazukan Jihar, tare da tukuicin tsauraran dokoki shida.
Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu, ya umarci dukkan wasu Fulani makiyaya da ke zaune cikin dazukan jihar (forest reserves), su fice daga cikin dajin nan da kwanaki bakwai.
Umarnin ko kuma dokar ya fara aiki ne daga ranar Litinin 18 Ga Janairu, 2021.
Akeredolu ya bada wannan umarnin ne a lokacin da ya yi ganawa tare da shugabannin Fulani makiyaya da kuma shugabannin kabilar Ebira da ke jihar.
Taron ya gudana a Babban Dakin Taro na Cocoa Conference Hall da ke cikin Gidan Gwamnatin Jihar Ondo a Akure, babban birnin jihar.
Akeredolu ya ce an dade ana fama da hare-hare da garkuwa da mutane wadanda wasu batagari ke yi da fakewa da kiwo amma su na garkuwa da mutane a jihar.
“A yau mun dauki babban matakin farko na dakile garkuwa da mutane da saukar manyan laifukan da ake aikatawa a fadin jihar nan.”
“Yawancin wadannan ayyukan garkuwa da mutane wasu batagari ne ke yin su masu fakewa da sunan makiyaya. Sun maida dazukan gwamnati wata mabuyar masu garkuwa da mutane, su na karbar makudan kudaden diyya.
“A matsayi na na Gwamnan Jiha wanda nauyin kare hakkin rayuka da dukiyoyin jama’a ke hannun sa, ina sanar da bijiro da wadannan ka’idojin da gaggawa, wadanda su ka hada da:
Tsauraran Dokoki 6 Da Gwamnatin Ondo Ta Kakaba Wa Makiyaya:
1. Makiyaya su gaggauta ficewa daga dukkan dazukan gwamnati da ke cikin jihar Ondo, nan da kwanaki bakwai, daga ranar Litinin 18 Ga Janairu, 2021 za su fara kirgawa.
2. An haramta kiwo cikin dare, saboda yawancin gonakin da makiyaya ke cinye wa amfanin gona, duk da dare ake yin aika-aikar.
3. An haramta zirga-zirgar shanun kiwo a kan manyan titina da kuma cikin gari.
4. An haramta kiwo ga duk wani yaron da ba balagi ba.
5. An umarci dukkan jami’an tsaron da ke Jihar Ondo su tirsasa bin wannan dokar tilas.
6. Amma gwamnatin mu mai tausayi ce, don haka duk wani mai son yin kiwo a jihar nan, to ya gaggauta yin rajista da hukumar da nauyin kula a kiwo ke kan ta.
Discussion about this post