A ci gaba da wasan kwallon kafa na kwararru a Najeriya, Enugu Rangers ta yi nasara akan Jigawa Golden Stars a garin Dutse da ci daya mai ban haushi.
Isreal Abia ne ya jefa kwallon a minti 79.
Haka aka yi doka ball, kamar za su ramu kafin alkalin wasa ya hura tashi amma inaa.
Yanzu kungiyar ƙwallon ƙafan Jigawa Golden Stars ce ta 12 a Tebur.
Ita kuma Enugu Rangers na na 8 a tebur.
Kungiyar Kano Pillars ta buga kunnen doki da Nasarawa United a garin Nasarawa.
A Katsina kuma, Katsina United ta doke Adamawa United da ci biyu babu ko daya. Sai kuma Plateau United da ta doke Hearthland da ci 3 babu ko daya a garin Jos.
Discussion about this post