#EndSARS: Minista Lai ya fassara ‘kisan Lekki’ da kisan da babu gawa ko daya

0

Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ya ragargaji Kotun Duniya ta Kasa-da-kasa saboda kiran da ta yi a yi binciken aikata laifukan yakin da ta ce jami’an tsaron Najeriya sun aikata kana bin da kotun ta kira “kisan kiyashin Lekki.’

A cikin hirar sa manema labarai ta farko cikin 2021 da ta gudana a ranar Litinin a Lagos, ya ce wannan bambarma da Kotun Duniya ta Kasa-da-kasa (ICC) ta yi, abu ne da aai iya kashe guyawun sojojin Najeriya masu yaki da Boko Haram da ’yan bindiga.

“Yayin da zaratan sojojin Najeriya masu kishin kasa ke ci gaba da yaki da masu garkuwa da Boko Haram, sai ita kuma kotun ICC da kungiyar Jinkai ta Duniya da wasu burbushin kungiyoyi su ka maida kan su wasu dakarun yaki da Najeriya.

“Wannan kungiyoyi ba su komai sai ci gaba da yaki sojojin Najeriya, tare da yi masu barazanar maka su kotun duniya bisa zargin yi wa mutane kisan kiyashi.

Lai ya bayyana cewa ICC da Amnesty International da sauran kungiyoyin da su ka soki salon yadda Gwamnatin Buhari ke tafiyar da batun ‘yancin dan Adam, cewa dukkan su barazana ce ga tsaron kasar nan.

“Najeriya ba ta shiga cikin kungiyr ICC domin a rika raina wa gwamnatin ta hankali ba. har yanzu mun rasa dalilin yadda irin wadannan kungiyoyi ke yi wa Najeriya ba jami’an tsaron ta barazana ba, a halin da sojojin kasar ke fama da masu ta’addanci da kuma masu garkuwa da mutane ba.”

“Ya kamata ICC da Amnesty International da ma sauran tarkace irin su su sani cewa su daina yi wa jami’an tsaron mu barazana, domin kara jefa kasar nan cikin bala’i su ke yi. Ya isa haka nan. Abin bakin ciki ne ganin yadda sau da yawa wadannan kungiyoyi ke gaskata labarai na bogi da na kiyayya da na adawa kan gwamnatin Najeriya. Har ta kai an sayar masu labarai na bogin karyar cewa an karkashe jama’a a Lekki, amma har yau an rasa gawarwaki.”

Share.

game da Author