Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi maraba da zaratan mata sojoji da rundunar Sojojin Najeriya suka aika hanyar Abuja-Kaduna don aikin gamawa da ƴan bindiga da suka addabi titin Abuja-Kaduna.
Rundunar sojin Najeriya ta aika da zaratan sojoji mata 300 zuwa Kaduna.
Zaratan mata sojojin zasu yi aiki tare da sauran jami’an tsaron da ke aikin samar da tsaro a wannan hanya.
Bayan haka ya jinjina wa rundunar sojoji
da wannan kokari da kuma huɓɓasa da suka yi na kara yawan jami’an tsaro a wannan titi yana mai cewa nan ba da dadewa ba hare-hare da yin garkuwa da mutane zai zama tarihi a wannan hanya.
Shugaban rundunar sojoji dake Kaduna Mohammed Usman ya godewa gwamnan jihar Kaduna El-Rufai da mataimakiyarsa Hadiza Balarabe na zuwa da kansu tarban wadannan sojoji da kuma gudunmawar da jihar ke ba sojoji dake aikin samar da tsaro a jihar.
Hanyar Abuja-Kaduna yayi kaurin suna wajen hare-haren ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Matafiya da dama sun gwammace su bi jirgin kasa maimakon su bi wannan hanya ko kuma idan suka rasa jirgi su hakura da tafiyar saboda rashin kwanciyar hankali.