Duk da rufe kan iyakoki, Najeriya ta shigo da abincin naira tiriliyan 1.85 cikin 2020 – Salami

0

Shugaban Kamitin Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tattalin Arziki, Doyin Salami, ya bayyana cewa duk da gamnatin tarayya ta kulle kan iyakokin ta tun daga Agusta 2019, hakan bai hana an shigo da kayan abinci kasar nan a cikin 2020 har na naira tiriliyan 1.85 ba.

Salami ya yi wannan ikirari a taron Manyan Masanan Harkokin Hada-hadar Bankuna na Najeriya, a ranar Talata.

“ Duk da rufe kan iyakoki da aka yi, an shigo da kayan abinci cikin kasar nan ya kai na kimanin naira tiriliyan 1.85 tsakanin watannin Janairu zuwa Satumba, 2020.

“Wannan adadin kudade sun ma karu da kashi 62 bisa 100 idan aka kwatanta da kudin da aka sayo kaya daga waje, a cikin 2019. Haka ya bayyana.

“Wannan ya nuna har yanzu mu na da raunin iya ciyar da kan mu a kasar nan, ba tare da mun dogara da abincin kasashen waje ba.

“Don haka akai bukata matuka a sake duba shirin tallafin harkar noma da tsarin bunkasa harkokin noman kacokan a Najeriya.”

Ya kara da cewa sannan kuma sauyin yanayi ya shafi manoma da yawan gaske a kasar nan, inda akalla manoma miyan 2.5 su ka hadu da ibtila’in ambaliya a 2019.

“Sannan kuma wani kalubale shi ne yadda a yanzu dala daya ya kamata a ce daidai ta ke da naira 439 a farashin gwamnatin tarayya”.

“ Sannan kuma barkewar cutar korona ya maida hannun agogon tattalin arziki baya da kusan shekaru 12 ba mu fuskanci kunci kamar na shekarar 2020 ba.

“ Bugu da kari kuma, banda wadannan kalubale, ga tattalin arzikin Najeriya na gwada kwanji da gugar kafada da matsallar rashin tabbas, cakirewar tattalin arziki, tsadar rayuwa, yawan jama’a a cikin gidaje barkatar da sauran matsaloli.” Cewar Salami.

Bangarorin da ya bayyana kullen korona ya shafa sosai, sun hada bangaren harkokin sufuri, bangaren harkar danyen man fetur da sauran su.

Share.

game da Author