Wata tsaleliyar mata ‘yar kasar Amurka mai suna Bea Lewis ta tona wani soyayya da ta yi da Hamshakin Attajiri, Aliko Dangote a Kasar Amurka, wanda ta ce ya ce amanar ta da soyayyar da ke tsakanin su sau dubu-dubu.
Bea Lewis ta saka hotunan ta da Dangote rungume da juna, sannan ta rubuta cewa Dangote ya rika wulakantata akai akai fiye da sau dudu-dubu, sai dai kuma ta amfana da shi matuka domin a zamanta da shi ta fahimci harkar kasuwanci, tattali da tsananta yin hakuri.
” Hira kawai da na rika yi da attajiri irin Dangote, fitacce a duniya yakan kwantar min da hankali. Sannan kuma na koyi abubuwa da dama a rayuwa, kuma na samu daukaka da arziki masu yawa.
Lewis ta kara da cewa a dalilin Dangote, ta daina aikin saida tuwo-tuwo, ta fada harkar siyan hannayen jari, sannan kuma ta mallaki gidaje biyu nata, kuma ta dilmiya cikin harkar kasuwanci gadangadan.
” Wani abu da na koya a zama na da Dangote shine yadda ya rika tausa ni yana min khuduba da in rika hakuri a cikin al’amurorina, in rika kama kai na da kuma yin tawali’u a koda yaushe.
A karshe, PREMIUM TIMES ta nemi ji daga bakin kakakin rukunin Kamfanonin Dangote ko sun san da wannan magana amma hakan bai yiwu ba, basu amsa waya ba.
Discussion about this post