Tun ana ganin kaman suratai kawai shugaban ƙasar Amurka Donald Trump yake yi, da ya ke ta kiran mutanen kasar musamman magoya bayan sa su fito su nuna kin amincewar su da nasarar da jam’iyyar ‘Democrat’ ta yi a zaɓen Amurka, a yau Laraba hakan dai ta tabbata.
Dubban magoya bayan Donald Trump sun kutsa majalisar ƙasar inda suka tarwatsa ƴan majalisar da ke zaman rattaba hannu a sakamakon zaɓen da aka gudanar a ƙasar a watan Nuwamba wanda Trump ya sha ƙasa.
Magoya bayan Trump sun kutsa cikin majalisar kasar dake Washington wato Capitol, su ka fatattaki ƴan majalisan sannan suka maye gurbin su da karfin tsiya da ƴan takife wasu a tube babu riguna a jikin su sannan dauke da rantama rantaman gorori.
Sun kukkutsa ofisoshin shugabannin majalisar, har da ofishin kakakin majalisar inda suka zazzauna abinsu suna ta daukan hotuna.
Ƙasashe da dama sun yi tir da wannan abu da ƴan Amurka suka yi ganin su ne ake koyi da musamman idan maganan Dimokradiyya ake yi a duniya.
Zaɓaɓɓen shugaban kasan Joe Biden ya yi kira ga Trump da kakkausar murya cewa ya fito yayi wa magoya bayan sa jawabi su shiga taitayin su.
” Wannan abin kunya har ina, ace wai yau Amurka ce ta watse haka tana malala abin kunya duk duniya a na gani. Dole Trump ya fito yayi wa magoya bayan sa jawabi su daina abinda suke yi tunda wuri”.