Ganin yadda cutar korona ta sake dannowa gadan-gadan a Najeriya sannan da yadda mutane ke bijire wa kiyaye dokokin gujewa kamuwa da cutar gwamnatin jihar Adamawa ta saka dokar hana walwala a jihar.
Bisa ga wani takarda da sakataren yada labarai na gwamnan jihar Ahmadu Fintiri, Humwashi Wonosikou, ya fitar ranar Talata a Yola gwamna Fintiri ya ce daga yanzu gwamnati ta hana taron mutane a duk fadin jihar.
Fintiri ya ce da gaske ne cutar korona ta bullo a kasar nan kuma cutar ba ta yi wa mutane da wasa.
” A Saka takunkumin fuska, a rika wanke hannaye da ruwa da sabulu, a rika goge hannaye da man tsaftace hannu, a daina gwamatsuwa wuri daya, da sauran su.
“A dalilin haka nake tunatar wa mutane cewa dokar hana walwala da gwamnati ta saka tun a watan Maris 2020 zai ci gaba da aiki.
“Gwamnati ta kuma hana taron mutane na kowani iri na sama da mutum 50.
Sannan duk gidajen holewa da shakatawa da aka kama ya tara mutane sama da 50 za a rufe shi.
Ya ce gwamnati ta saka dokar hana mutane yawo a jihar daga karfe 10 na dare zuwa biyar na safe.
Fintiri ya yi kira ga duk malaman adini da su ba gwamnati goyon baya domin mutane su kiyaye dokokin da aka saka.
Ya ce gwamnati za ta saka jami’an tsaro domin tilasta mutane bin wadannan dokoki.
Zuwa yanzu mutum 424 sun kamu a jihar, mutum 283 sun warke, 161 na kwance a asibiti sannan 25 sun mutu.Mutum 91,351 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 75,699 sun warke, 1,318 sun rasu.Sannan kuma zuwa yanzu mutum 14,267 ke dauke da cutar a Najeriya.