Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bada umarnin kwac dukkan kudaden da ke cikin asusu daban-daban na tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari.
Kotu ta ce kwace dukkan kudaden ya zama wajibi, saboda tsohon gwamnan, kuma tsohon shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya tsakanin 2015 zuwa 2019, ya kasa yi wa kotun sahihi kuma gamsasshen bayanin yadda ya mallaki makudan kudaden.
Yawancin kudaden dai an dankare su ne a Bankin Polaris, kamar yadda aka fitar da bayanai dalla-dalla.
An kwace masa dalar Amurka 56,056.75 a asusun Polaris Bank, sai kuma naira milyan 12.9 da kuma wasu naira milyan 11.2.
Akwai kuma wasu zunzurutun dalolin Amurka ajiye har dala 301,319.99 wadanda su ma kotu ta kwace.
Sannan an kwace naira 217,388.04, sai kuma wasu dala 311,872.15 da ya boye a Zenith Bank, wadanda su ma kotun ta kwace daga hannun sa.
Babbar Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu, ta ce kotu ta kwace kudaden kamar yadda EFCC ta roki kotun ta yi, tunda Yari ya kasa bada kwakkwaran bayanin yadda ya tara kudaden, a matsayin sa wanda ba dan kasuwa ba.
Yari ya yi gwamnan Zamfara tsawon shekaru takwas, daga 2011 zuwa 2019.
Tun da farko dai ICPC ce ta shigar da kara tun cikin 2019, inda ta shaida wa kotu cewa sun gano inda Yari ya boye wasu makudan kudade. Don haka ICPC ta na bukatar kotu ta kwace kudaden, ko kuma Yari ya je ya yi wa kotu gamsasshen bayanin hanyar da ya bi ya samu kudaden.
Hukumar ICPC a lokacin ta maka Yari kotu tare da wasu kamfanonin sa biyu, wato Kayatawa Nigeria Ltd da kuma B. T. Oil and Gas Nigeria Ltd.
Tun a ranar 16 Ga Agusta, 2019 ce Mai Shari’a Taiwo Taiwo ya bada umarnin a kulle asusun kada a bar Yari ya kara taba ko sisi a cikin kudaden, har sai an ga abin da shari’a ta kaya tukunna.
Lauyan ICPC Osuobeni Akponimisingha ne ya shigar da karar Yari a madadin ICPC.
A lokacin mai shari’ar ya kuma yi wa Yari adalci cewa duk ma wani da ke ganin cewa kudin da ke asusun Yari na sa ne, to ya zo kotu ya bayar da shaida. Amma ba a samu ko mutum daya ba.
ICPC ta ce kudaden da ke asusun Yari duk na sata ne, kudade ne mallakar al’ummar jihar Zamafara da kuma Gwamnatin Tarayya.
Shi dai Yari ya kasa kare yadda aka yi ya tara kudaden, sai dai kawai ya ce wa kotu shi fa tun kafin ya zama gwamna kasaitaccen attajiri ne.