Dalilin da ya tantabaru su ka kunyata Buhari a ranar Tunawa da Mazan Jiya

0

Wannan ne karo na biyu da tantabarun da Shugaba Muhammadu Buhari ke saki, domin su tashi sama, su ka ki tashi.

Tashin tantabarun dai na nuni da cewa akwai zaman lafiya da lumana da kwanciyar hankali a cikin kasa.

A ranar Juma’a a wurin Bikin Tunawa da Mazan Jiya, wato sojojin da suka kwanta dama a wajen kare kasa, tantabarun da Buhari ya saki sun ki tashi.

Lamarin ya faru ne a Dandalin Eagle Square, wanda bayan an bude su a cikin wani kejin da aka yi wa fenti launin fentin Najeriya, tantabara ta farkon da Buhari ya saki da kuma sauran duk su ka ki tashi.

Tuni dai a soshiyal midiya jama’a ke ta tofa albarkacin bakin su dangane da kin tashin fararen tantabarun.

Buhari ya halarci bikin tare da Mataimakin sa Yemi Osinbajo.

Sojoji sun yi jerin kwago da fareti, kuma an yi kidan badujala. Sannan Buhari ya nufi kejin domin ya bude tantabarun.

Ganin an bude tantabarun amma sun ki tashi sama, sai Buhari ya dauki daya, ya cilla a sama. Amma maimakon ta tashi sama, sai ta yi kememe, ta dira a kan kejin.

Sai dai kuma daga baya, bayan Shugaba Buhari ya koma wurin zaman sa, antabarun sun tashi sama abin su.

Wannan dai wata al’ada ce da cake yi duk shekara, mai nuna cewa ana zaune lafiya a cikin kasa.

Wani likitan dabbobi da tsuntsaye mai suna Barnabas, ya ce wannan ba wani abu ba ne, domin watakila tantabarun sun dade a cikin kejin, kuma sun saba rayuwa a ciki, shi ya sa su ka ki tashi.

A cikin 2019 ma tantabaru sun yi wa Buhari haka, kamar yadda shi ma tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya saki na sa a 2014, amma su ka ki tashi.

Share.

game da Author