Gwamnan Jihar Jigawa Abubakar Badaru ya bayyana cewa zumunta da kusancin sa da gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya sa ya gayyaci zuwa Jigawa ya kaddamar da wasu ayyuka da gwammanatin sa aiwatar.
Badaru ya kara da cewa shi mutum ne da yake daraja zumunci da abokantaka mai karfi, ” Shine ya sa na gayyaci aminina tambuwal ya zo Jigawa ya kaddamar da wasu ayyuka da muka yi.
” Domin ba mu jam’iyya daya shi kenan kuma sai ace wai ba za muyi zumunta ba. Wannan shine dalilina na gayyatar sa jihar Jigawa ya kaddamar da ayyukan ci gaba da muka yi.
Sai dai kuma wadanda ba su ga maciji da gwamnan jihar, musamman ‘yan jam’iyyar APC sun koka kan yadda gwamnan ya fifita gwamnan PDP fiye da na APC da suke birjik a kasar nan.
” Maimakon ya gayyaci wani gwamnan APC sai ya gayyaci gwamnan jam’iyyar adawa, hakan da yayi ya nuna mana cewa akwai wani abu a kasa da ake girkawa ba mu sani ba amma dai muna nan mun kimshe muna sa ido muka yadda za ta kaya.”
Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar, Faisal Jazuli, bayyana cewa abin da Badaru yayi ya tada hankalin ‘yan jam’iyyar APC a jihar kuma ya tabbatar musu cewa da gaske Badaru yake ya rugurguza jam’iyyar kafin ya karkada ya yi tafiyar sa a 2023.