Dalilin da ya sa Buhari za a fara yi wa rigakafin Korona – Faisal Shu’aib

0

Gwamnatin Tarayya ta roki ƴan Najeriya su daina tsoro ko ƙin yarda da allurar rigakafin cutar korona.

Shugaban Hukumar Kula Da Lafiya A Matakin Farko (NPHCDA), Faisal Shuaib, ya ce idan aka shigo da allurar rigakafi a kasar nan, to Shugaba Muhammadu Buhari, Mataimakin sa Yemi Osinbajo da sauran manyan kasar nan ne za a fara yi wa allurar domin a karfafa wa jama’a guiwar amincewa a yi masu allurar.

Shuaibu ya ce Buhari da Osinbajo duk sun amince za a yi masu allurar rigakafin korona kai-tsaye a nuna lokacin a gidajen talbijin, domin a karfafa zukatan ƴan Najeriya su karbi allurar hannu bibbiyu.

Haka dai shugaban na NPHCDA ya bayyana ranar Alhamis a Abuja, loakacin da kwamitin yaki da cutar korona ke ganawa da manema labarai.

Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito cewa Najeriya ta kudiri aniyar yi wa akalla mutum milyan 42 allurar rigakafin cutar korona.

Hakan na nufin kenan za a yi wa kashi 1 bisa kashi 5 na yawan ‘yan Najeriya wannan allura kenan.

Wadannan ruwan allura dai ana sa ran za a samu nasarar dankara wa akalla kashi 40 bisa 100 na ƴan Najeriya allurar korona cikin 2021 sai kuma wasu kashi 30 bisa 100 cikin 2022.

Ana sa ran Najeriya za ta samu kwalaben allurat rigakafin korona guda 100,000 a karshen watan Janairu, 2021 din da mu ke ciki.

Shuaib ya ce Shugaba Buhari da Yemi Osinbajo da kuma wasu manyan Najeriya duk sun nuna amicewar su cewa su na a sahun farko na ‘yan Najeriya da za a fara dankara wa allurar rigakafin cutar korona a Najeriya.

“Wadannan shugabanni duk sun amince za a yi masu allurar kai-tsaye a nuna a gidan talbijin domin a kara wa ‘yan najeriya kwarin guiwar su yarda kuma su yi amanna da allurar rigakafin.

Share.

game da Author