Dakarun rundunar Hadarin Daji sun hallaka ƴan ta’adda 50 sun kwato dabbobi da dama a Zamfara

0

Kodinaton yaɗa labarai na rundunar Sojojin Najeriya, John Enenche ya bayyana cewa dakurun soji dake aiki karkashin rundunar Hadarin Daji, sun kashe masu garkuwa da mutane akalla 50 a harin da suka kai musu ranar Lahadi.

Enenche ya kara da cewa an yi wa maharan shugan bazata ne, ana yi musu luguden wuta ta sama sannan ta kasa kuma sojojin kasa na karisa. Sannan an kwato dabbobi sama da 270 a wannan hari da aka kai dajin.

Bayan haka kuma ya ce dakarun ba su tsaya nan ba, sun kutsa can cikin dajin har zuwa kauyen Dunya dake karamar hukumar Ɗanmusa inda suka kwato dabbobi 62 daga hannun wasu mahara da suka arce a lokacin da suka hango jami’an tsaro na sintiri a kauyen.

A karshe Enenche ya ce ana ci gaba da jinjina wa sojojin kan sadaukar da ransu da suke yi.

Share.

game da Author