Cin Kwai ya kusa gagaran ƴan Najeriya muddun gwamnati bata waiwayi fannin ba – Kungiyar masu kiwon kaji

0

Tsananin tsadar waken soya da masa ya sa nan bada dadewa ba gaba daya cin kwai zai gagari ƴan Najeriya.

Babban sakataren kungiyar na yankin Kudu Maso Yamma ya ce muddun gwamnati ba shigo cikin wannan al’amari ba ta kawo wa mutane dauki cikin gaggawa ba, to baya ga karancin kwai da za a samu, mutane sama da miliyan 10 za su rasa aikin yi.

Ya ce daga watan Afrilun 2020, abincin kaji ya yi tashin gwaiton zabi har sau uku akasar wanda yasa baya ga kwan da yayi tsada su kan su kajin sun yi tsada.

Yanzu kiret din kwai yakai naira N1300 daidai da kusan mudun shinkafa kenan.

Odunsi ya ce lallai idan ana so a ceto wannan wannan fanni dole sai gwamnatin tarayya ta bada dama a shigo da masara da waken soya, in ba haka ba kuwa akwai wawukeken matsala da za a fada ciki na rashin kwai da kajin kan su.

A sanadiyyar tsadar abincin kaji, ga kuma tsananin talauci da ya addabi mutane, wasu da dama ba su iya cin kaji a lokacin Kirsimeti ba, sabida da tsadar kaji zaka ji ko da abincin da za aci za ka ji da.

A karshe dai ƙungiyar manoman sun koka ba gwamnati shawarar ta karkato da akalarta zuwa wannan bangare tun da wuri, ta saka hannu sosai sannan ta bada dama a shigo da masara da waken soya.

Share.

game da Author