CASUN NUNA TSIRAICI DA TAMBADEWA: Mai Otel din ‘Asher’ ta yi barazanar maka El-Rufai a Kotu

0

Aisha Yakubu, mamallakiyar Otel din Asher dake unguwar Sabon tasha dake Kaduna ta yi barazar maka gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai a Kotu a cewarta wai babu-gaira-babu-dalili yin haka.

Ta ce tana ci gaba da tattaunawa da makusanta domin yiwuwar maka gwamnatin Kaduna a Kotu kan rusa mata Otel din ta da gwamnatin jihar tayi a dalilin zargin za a yi casun nuna tsiraici da tambadewa a Otel din.

Idan ba a manta ba Rundunar ‘yan sandan Kaduna ta kama matasan da suka shirya sharholiyar gwangwajewa tsirara a Kaduna ranar 27 ga Disamba.

Wasu matasa sun shirya bikin sharholiya da fasikanci tsakanin mata da maza a garin Kaduna domin murnar karshen shekara.

Matasan sun saka katin gayyata da tallata sharholiyar a shafin Facebook, inda suka saka wasu sharudda da suka hada da wai duk mai son halartar gwangwajewar ya zo wurin babu kaya a jikin sa, wato tsirara haihuwar uwar sa.

Bayan nan ya tabbata ya zo da kororo roba, domin za a tafka fasikanci ne tun daga karfe 8 na dare zuwa washe garin ranar 28.

Domin shiga wurin gwangwajewar, mai bukatar haka zai biya naira 1000, sannan akwai wurare na musamman da za a biya naira 2000 zuwa naira 5000.

Sai dai kash, wannan haka ta su bai kai ga ruwa ba, domin jami’an tsaro sun farwa masu hada wannan shu’umanci inda suka bi sahun su har Allah ya sa suka damke wasu saga cikin masu shirya wannan sharholiya.

Daya daga cikin maiba gwamnan Kaduna shawara kan harkokin yada Labarai, Abdallah Abdallah, ya rubuta a shafinsa ta tiwita cewa yayi matukar farin cikin damke wadannan yara da aka yi.

Mazauna Kaduna kuma sun yi tofin Allah-Tsine ga wadanda suka shirya wannan biki, suna masu godewa jami’an tsaro kan saurin kama wadannan yara da suka yi.

Zan garzaya kotu

Aisha ta ce bata sanda wannan shiri na yin bukun nuna tsraici ba, sannan ta yi wa ‘tan sanda suk bayanin da suke so a lokacin da suka zo yin bincike kan wannan Zargi.

” ‘Yan sanda sun bi diddigin abin, sun gayyace har ofishin su kuma sun bukaci in basu kudi. Sai da na biya kudin belin wani da aka kama a kulle da akan wannan zargi har naira N100,000. A jikin wannan katin gayyata da aka manna a ko-ina babu inda aka saka cewa wai a Otel dina za a yi wannan buki.

Aisha ta kara da cewa ko da aka kamo wadanda ke shirya wannan biki basu shaida cewa wai a otel dinta za su yi wannan biki na ashararanci ba.

” Baya ga ginin Otel dina da na rasa, na rasa kayan ciki duka domin babu shiri aka rusa ginin da komai da ke ciki. Zan garzaya kotu domin a bi min hakki na.”

Share.

game da Author