Bunkasar noman masara a Najeriya daga 1960 zuwa yau

0

A yau Najeriya na noma masarar da ta nunka wadda ta ke nomawa a 1960 har nunki 10. Wannan shekara ta 1960 dai ita ce shekarar da Najeriya ta samu ’yanci. Hukumar Bunkasa Noma ta Amurka (USDA) ce ta fitar da wannan kididdiga.

Sai dai kuma duk da kasancewa Najeriya ita ce kasa ta biyu da ta fi noma masara mai yawa a Afrika, manoman kasar nan sun koka cewasu na tsoron shigo da masara mai saukin farashi daga wasu kasashen Afrika zuwa cikin Najeriya zai iya karya kasuwar masara a kasar.

Sannan kuma su na fargabar cewa masarar da ake nomawa a cikin Najeriya, ba ta za yi tsiri a kasuwannan kasashen Afrika ba.

Hukumar USDA ta binciko cewa masarar da ake nomawa a Najeriya na nunkawa a duk shekara, tsakanin 1999 zuwa 2019. Sannan kuma adadin yawan wadda ake nomawa cikin shekaru biyar da su ka gabata, shi ne adadi mafi yawan masarar da aka noma a kasar nan.

Yawan masarar wadda aka noma tsakanin 2014 zuwa 2019 ne ya kai Najeriya zama kasa ta biyu mafi yawan kasashe masu noma masara a Afrika.

Ratar Yawan Noman Masara Tsakanin Gwamnatin Buhari da Gwamnatocin Baya

Cikin wadannan shekaru Afrika ta Kudu wadda ita ce kasa mafi karfin noman masara mai yawa a Afrika. Ta noma mitrik tan milyan 12.9 a wadannan shekaru biyar daga 2014 zuwa 2019. Ita kuma mai bi mata wato Najeriya, ta noma metric tan na masarar milyan 10.2.

A 2017 ta noma mtm 10.4, sai kuma ta kara noma mai yawan mtm 11.0 cikin 2018. Kuma wannan adadin ta noma cikin 2019.

Yawan masarar da Najeriya ke nomawa ya rika karuwa daga mtm 10.1 cikin 2014, mtm 10.6 cikin 2015 da kuma 11.mtm cikin 2016.

A karkashin shekaru biyar na Gwamnatin Buhari, akalla kowace shekara ana noma masara mtm 10.8. Amma idan aka kwatanta da gwamnatin Ollusegun Obasanjo, Musa Yar’Adua da Goodluck Jonathan, za a ga cewa an rika noma mtm 5.5, 7.3 da kuma 9.0 a gwamnatocin daki-daki.

A Najeriya dai kasar da ta kowace kasa yawan al’umma a Afrika, cikin 1960 an noma masara tan 914,000. Amma cikin 2019 an noma har metric tan milyan 11.0.

Tasirin Shirin Ramcen Kudaden Noma (Anchors Borrowers’ Programme) Ga Noman Masara

Shugaban Kungiyar Manoma Masara ta Kasa (MAGPMAN), Uche Edwin, ya danganta bunkasar noman masara mai tarin yawa a karkashin gwamnatin Buhari da dalilin shigo da tsarin Lamunin Noma na ‘Anchor’s Borrowers’ Programme’ (ABP) da Gwamnatin Buhari tacshigo da shi.

“Yanzu ka ga cikin 2020 kadai Shirin ABP ya bunkasa manoma 150,000 da llamunin noma. Wannan ya taimaka wajen inganta kayan fasahar noma na zamani domin tallafawa ga kananan manoma.” Inji Edwin.

Sai dai kuma Edwin ya ce akwai bukatar Najeriya ta kara yawan masarar da ta ke nomawa din domin cike gibin da ya rage.

Cikin Nuwamba 2015 ne Shugaba Muhamadu Buhari ya kaddamar da Shirin Baiwa Manoma Ramce na ABP, da nufin bunkasa noma a kasar nan.

Shirin ya maida hankali ne wajen rage dogaro da shigo da abinci daga waje.

An rika bada ramce ga manoman shinkafa, masara, alkama, auduga, doya, rogo, rake, tumatir, kiwon dabbobi da sauran su.

Yadda tsarin ya ke shi ne, idan manomi ya noma amfanin gonar sa, zai dauka ya kai wurin da za a zame adadin kudin da ya ramta kawai ba tare da jekala-jekala ba.

Edwin ya ce kafin shigo da tsarin ABP, masarar da aka noma a 2013 a kasar nan ba ta wuce mtm 7.3 ba. Amma shigo da tsarin ABP ya sa a cikin 2019 an noma mtm 10.1.

“Mu na sa ran a cikin 2021 za a iya noma mtm har milyan 20 zuwa milyan 21.” Inji Edwin.

Bude Kan Iyakoki Zai Karya Manoman Masara –Cletus

Sake bude kan iyakoki da aka yi zai kawa wa noman masara cikas. Hada dai wani babban mai sarrafa kayan noma na kamfanin Greeen Grass Intercontinental Synergy ya bayyana wa PREMIUM TIMES.

“Saboda ‘yan Najeriya sun sayi kayan noma da tsada, domin a tunanin su, a kasuwannin Najeriya ne kadai za su yi cinikin su, tunda an rufe kan iyakoki.

“Amma ka ga kenan akwai matsala tunda a yanzu an bude kan iyakoki.”

“Yanzu ka ga a shekarun baya ana saida buhun masara naira 5000 zuwa naira 7000. Ya danganta ga garin da kasuwar masarar ta ke.

“Amma a wannan shekarar a cikin Oktoba zuwa Nuwamba, sai da buhun masara mai nauyin 50kg ya kai har naira 12,000. Dokar kulle da kuma annobar korona ce ta kawo wannan tsadar.”

Sai ya ce amma sake bude kan iyakoki zai na ‘yan kasuwa damar shigo da masara mai saukin farashi, wadda za ta karya kasuwar masarar da aka noma cikin Najeriya kenan.

Ya nuna rashin jin dadin cewa hakan zai tilasata wa manoman masara a Najeriya su saida masarar su da arha, alhali sun sayi kayan aiki da kayan noman su da tsada.

“Gaskiyar magana guyawun manoman masara a kasar nan da dama sun yi sanyi ganin da su ka yi an sake bude kan iyakoki. Saboda sun sayi kayan noma da tsada, kuma sun yi noman da tsada. A tunanin su za su maida kudin su har su ci riba a nan cikin gida, tunda han rufe kan iyakoki.

“Amma yanzu da aka bude kan iyakokin nan, tilas abin zai shafe su, domin masarar da aka noma cikin gida za ta karye a kasuwa, a bar su cikin gagarimar asara kenan.” Inji Aneke.

Share.

game da Author