Shugaba Muhammadu Buhari ya zargi manyan Najeriya da ke ragargazar gwamnatin sa ido-rufe, duk kuwa da dimbin nasarorin da ya ce gwamnatin ta sa ta samar a kasar nan.
Buhari ya yi wannan jawabi a ranar Asabar, bayan da ya sabunta rajistar sa ta zama cikakken dan jam’iyyar APC, a garin Daura, jihar Katsina.
An nuno Buhari ya na rubuta sunan sa a kan sabuwar rajistar jam’iyyar APC a tsakiyar manyan ‘yan jam’iyyar APC da su ka hada da gwamnoni, ba tare da ya daura takunkumin baki da hanci, maganin kamuwa ko baza cutar korona ba.
Sannan kuma ya gode wa Kwamitin Rikon Jam’iyyar APC, bisa ga karfi-halin iya rikon jam’iyyar da su ka nuna, kuma su ke kan yi.
Shugaba Muhammadu Buhari ya zargi manyan Najeriya da ke ragargazar gwamnatin sa ido-rufe, duk kuwa da irin kokarin da gwamnatin ke yi wajen “farado da darajar danyen mai da sauran dimbin nasarorin da ya ce gwamnatin ta sa ta samar a kasar nan.
“Lokocin da mu ka karbi mulki, yawan danyen mai da ake hakowa a kasar nan bai kai ganga rabin milyan ba. Sannan sai da muka ceto jihohi da kudaden da su ke iya biyan albashi.
“Haka muka rika agamniya a gaganiyar nemo kudaden da za mu rika biya. Duk kuwa da makudan kudaden da aka samu daga 1999 zuwa 2014, sai da mu ka rika bai wa jihohi kudade su na biyan albashi. Amma duk da wannan kokari da mu ka yi, manyan ‘yan bokon kasar nan ba su ganin kokarin mu. Sai dai kullum ragargazar gwamnatin mu su ke yi.
‘Ku da ke cikin mazabun ku, akwai aikin da ya wajaba a kan ku, wato ku rika jan hankalin wadannan manyan ‘yan boko cewa don Allah su rika girmama mu da kuma mutunta mu ta hanyar da mu ka yi ayyukan raya kasa da dan abin da ke hannun mu”. Haka Buhari ya shaida wa wadanda su ka halarci wurin da ya sabunta rajistar.
Buhari ya nuna cewa Shugaban Riko na APC kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mala Buni, shi ne mutumin da ya fi cancanta ya rike shugabancin APC.
Ya cewa Gwamna Buni ya fi shi Buharin kan sa sanin halin da APC ke ciki, a matsayin sa na wanda ya taba dadewa kan mukamin sakataren jam’iyyar.
Discussion about this post