Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai kan wadanda su ka kashe mutane 70 a garin Zaroumdareye, kan iyakar Nijar da Mali.
Ya bayyana kisan a matsayin wani babban dalilin da ya wajaba kasashe su hada karfi wuri daya domin su dakile ta’addanci dungurugum.
Da ya ke nuna damuwa kan wannan mummunan kisa da aka yi a ranar Lahadi, Buhari ya ce, “Abin ya tayar min da hankali matuka, jin irin yawan mutanen da masu ta’adddar su ka kashe, saboda ba su dauki ran mutum da wata daraja ba.”
Sannan Buhari ya kara ca cewa, “Mu na fuskantar gagarimar matsalar tsaro ganin yadda masu ta’addanci ke ci gaba da burunkara a yankin kasashen Sahel. Saboda haka babu abin da zai iya kawar da su sai hada hannu wuri daya tsakanin kasashen, domin a kakkabe makiya kuma masu gaba da zamantakewar dan Adam a doron kasa.”
Ya kara da cewa. “A yanzu dai ta’addanci ya zama wata babbar masiba ko annoba mai zaman kanta, wadda a ko da yaushe ta iya fantsama, idan ba hada kai aka yi, aka fatattake ta a lokaci daya ba.”
Daga nan ya kara da cewa, “kasawar daya daga cikin kasashen Afrika ta magance matsalar tsaro, to abin zai shafi sauran kasashen.”
Sai kuma ya kara tunatar da cewa, “ruguza gwamnatin Libya da aka yi cikin 2011 ya haifar da gagarimar matsalar tsaro a kasashen Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi, kai har ma da sauran kasashe.”
” Daka wasoson dimbin makaman Libya da aka yi bayan faduwar gwamnatin Gaddafi ya haifar da safarar muggan makamai a hannun ‘yan ta’adda da mabarnata, wadanda a yanzu su ka zama barazana ga tsaron wasu kasashe da dama.” Inji Buhari.
” Ina mai mika ta’aziyya ta ga gwamnatin Nijar da al’ummar kasa da kuma iyalan wadanda su ka rasa rayukan su.” Inji Buhari.