Babban Alkalin zaben da ya hura usur din gwagwarmaya da fadi tashin da aka yi a zaben 2015 wanda ita ce ta kawo gwamnatin APC karkashin shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce lallai gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ba mutanen Najeriya kunya ‘ musamman wadanda suka rika tattada jijiyoyin wuya suna haki da ba hammata iska kan lallai sai wannan gwamnati ta dare kujerar mulki ko ta halin kaka domin talakawa su wataya.’
Buhari ya kunyata mutane da yawa a Najeriya. Sai dai Har yanzu yana da sauran lokacin da zai gyara kurajuren da ya yi idan har hakan ake so a yi. Amma gaskiya, gwamnatinsa ta kasance abin takaici sosai ga ‘yan kasa. Mutane da yawa sun yi masa fatan alheri, amma kuma yanzu ganin yadda al’amurorin kasar ke tafiya suna ganin akalar tafiyar ta karkata zuwa wani wurin daban.
” Gudanar al’amurorin gwamnati sun sukurkunce, sun lalace musamman a gwamnatin Tarayya da wasu Jihohin kasar nan. A kullum zaka ga abubuwa na ci gaba da ta tabarbarewa, Ta’addanci ne, Mahara ne, ‘Yan bindiga ne, ga kuma fashi da makami da dai sauransu duk sun yi kasar rawani a ka.
Jega ya kara da cewa dole ‘yan siyasa su rage son kai, satar kudin gwamnati da facaka da su.
Farfesan ya ce dole a samo matsaya daya gami da sake fasalin Najeriya kafin 2023, domin idan ba ahaka ba kuwa toh akwai sauran rina a kaba.
” Abinda nake ganin ya fi dace wa shine a rage wa gwamnatin Tarayya karfi, a kara wa jihohi karfi, kowacce jihar ta samu karfi da cin gashin kanta na iko da arzikin jihar ta.
A karshen hirar wanda Daily Trust ta wallafai a jaridar ta, Jega ya yi bayani game da wasu hanyoyi da za abi wajen kawo karshen yajin aiki da kungiyar malaman jami’o’i ke yi a kasar nan sannan kuma ya ce a 2023 ya kamata a duba dan takara da ya dace ne ya cancanta ba abi wani tsari na da ban ba.