Shugaba Muhammdu Buhari ya gargadi masu hankoro da tayar da jijiyarwuyan ruruta gabar addinanci da wutar kabilanci a fadin kasar nan.
Ya ce masu wannan mummunar aniya ba su kaunar Najeriya, kuma ba abin alheri ne su ke kokarin shukawa ba.
Ya kuma kara da cewa gwamnatin sa za ta ki gaba da tabbatar da cewa kowane mabiyin kowane addini ya samu sararin yin addinin sa cikin ‘yanci, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya shimfida.
Buhari ya yi wannan gargadi ne a lokacin da Majalisar Kolin Addinin Musulunci ta kai masa ziyara, a karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar lll.
“Gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da bayar da damar yin addini ga kowane dan Najeriya, kamar yadda doka ta tanadar.
“Amma kuma Gwamnatin Tarayya ba za ta kyale masu kokarin yin amfani da kabilanci ko adinanci su rura fitinna accikin kasa ba. Aiki na ne na tabbatar na yi wa kowane bangaren al’umma adalci.”
Buhari ya kara tabbatar wa tawagar da ta kai masa ziyarar cewa gwamnati za ta yi dukkan kokarin za ya kamata domin ganin ta dakile matsalar tsaro a kasar nan.
Daga nan sai ya yi kira ga mzauna karkara su rika taimaka wa jami’an tsaro wajen ganin sun gudanar da aikin tsaron kasa bakin kokarin su.
“Matsalar tsaron nan ta rike mana makogaro tamau, amma ai har yau ba mu nuna gajiyawa ba, kuma ba za mu taba nuna gajiyawa ba, har sai mun kakkabe wannan kalubale a kasar nan.
“Mu na kuma kara yin kira ga jama’ar karkara su kara tashi tsaye wajen kai wa jami’an tsaro bayani na sirri yadda za su kakkabe duk wata matsalar tsaro a yankunan su.”
“Na yi amanna cewa Gwamnati ce ke da nauyi da alhaki wanzar da zaman lafiya da samar da tsaro a kasa. To amma fa ba za ta iya wannan gagarimin aiki ita kadai ba, tilas sai da sa hannun irin ku.
“Saboda haka ina so ku rika ba jami’an tsaro rahotannin duk wata barazanar tsaro da ku ka ga kokarin kunno kai. Ta haka ne za a taru a magance matsalar baki daya.”
Sarkin Musulmi ya jinjina wa Buhari dangane da nasarar da ya ce an samu wajen samar da tsaro a Yankin Arewa maso Gabas.
Daga karshe sai ya yi kira ga shugaban kasar da ya gaggauta kawo karshen ‘yan bindiga a jihohin Arewa maso Yamma, wadda su ka hana jama’a zaman lafiya a jihohin Kaduna, Zamfara, Sokoto da Katsina har ma da jihar Neja.
Discussion about this post