BIDIYO: Kyautar motar da Rarara yayi wa Jamila Nagudu

0

Shahararren mawakin siyasa, mawakin Ganduje, Buhari, El-Rufai da Masari, Dauda Kahutu Rarara ya rabawa wasu daga cikin jaruman Kannywood sabbin motoci kyauta.

Wadanda Dauda ya baiwa sabbin motoci kirar Toyota Matrix suna hada da Jamila Nagudu da Tijjani Asase.

Wannan ba shi ne karon farko da shahararren mawakin ke yi wa abokan aikinsa goma ta arziki ba.

Sau da yawa a wasu lokuttan, sukan fito su yaba masa kan wani abin arziki da yayi musu.

A wani bidiyo da Darekta Aminu Bono da Ali Nuhu suka saka a shafukan su ta Instagram, an nuno jarima Jamila Nagudu cike da murna a lokacin da Rarara ya ke mika mata mukullin motar da ya siya mata.

Haka shima Tijjani Asase, ya karbi ta sa mukulli cike da farin ciki.

Abokanan aikin wadannan jarumai sun yi wa mawakin ambaliyar addu’o’in allah ya saka da Alkhairi.

Share.

game da Author