Wasu mahara da ake zaton Boko Haram sun kai hari garin Geidam a jihar Yobe.
Har zuwa lokacin da ake rubuta wannan labari da misalin karfe shida da rabi na yamma maharan da jami’an tsaro na ta batakashi a garin.
Mazauna garin da dama sun gudu cikin daji wasu kuma sun boye a cikin gidajen su gudun kada garin gudu kuma harsashi ya dauke mutum.
Wani mazaunin gari da ya zanta da PREMIUM TIMES a gigice ya ce barin wutan da maharan ke yi ya wuce misali ko a kwatanta shi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Abdulkarim Dungus ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa da ya kira DPO din ofisohin ‘yan sandan garin ya ji yana ta raba bindigogi.
“Ya ce zai kira ni a wayar salula anjima.
Geidam gari ne dake da nisan kilomita 200 daga Damaturu kuma garin na iyaka kasa da Jamhuriyyar Nijar.
Boko Haram sun dade suna kai wa garin hari inda a dalilin haka an rasa rayukan mutane da asarar dukiya da mai yawa.