Bankin FCMB na binciken Shugaban bankin kan zargin ya haifi ’ya’ya biyu da matar wani

0

Akalla mutum 1400 ne ya zuwa yanzu su ka sa hannu a kan takardar kiraye-kiraye ga Babban Bankin Najeriya, CBN cewa a kori Adam Nuru daga Shugabancin bankin FCMB.

Bukatar hakan ta taso ne bisa wani zargi da korafi da aka yi a rubuce cewa ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum mai suna Tunde Thomas.

An hakkake cewa Thomas ya mutu ne a ranar 16 Ga Disamba, sanadiyyar kududun bakin ciki da bugun zuciya, bayan da matar sa ta bayyana masa cewa, ’ya’ayan su guda biyu, ba na sa ba ne, domin ba cikin sa ba ne. Ta shaida masa kai-tsaye cewa ogan sa Adam Nuru, Shugaban Bankin FCMB na Najeriya, shi ne ya yi cikin yaron na farko. Sannan kuma shi ma dan na biyu, duk Nuru din ne ya dirka mata cikin ta haife su.

Cikin takardar korafin, an yi zargin cewa matar Thomas mai suna Moyo ta shaida masa cewa ga ta can ta kama hanyar zuwa Amurka tare da yaran su biyu.

An ce bayan ta isa Amurka, ta kira shi a waya tare da shaida masa cewa yaran nan fa biyu ba shi ne ya yi cikin su ba

Takardar korafin ta ci gaba da cewa bakin ciki ya sa Thomas ya samu cutar shanyewar rabin jiki, amma daga baya ya murmure, har ma ya fara neman auren wata mata.

“Tunde Thomas ya mutu makonni biyu bayan ya yi fama da matsananciyar damuwa.

“Saboda haka yaran nan biyu da matar sa Moyo ta haifa, ba na sa ba ne, ’ya’yan Adam Nuru ne, Shugaban bankin FCMB, shi ne farkan da ya rika neman ta, kuma ta haifi yaran biyu da shi.

“Tunde bai dade da zama darakta ba a FCMB. Makonni biyu da su ka gabata, ya koma gida daga wurin aiki, kawai sai ya yanke jiki ya fadi, ana sauran kwanaki biyu kacal a daura auren sa da budurwar sa, wadda a yanzu haka ta na dauke da cikin sa.

Takardar korafin ta yi zargin cewa Shugaban FCMB na ta kokarin binne maganar, domin kada abin ya fito fili har ya shafi aikin sa da mutuncin sa.

Tuni dai wani lauya mazaunin Akure, babban birnin Jihar Ondo mai suna Bolanle Cole, ya fara kamfen din neman babban Bankin Najeriya, CBN ya tsige Adam Nuru daga shugabancin ‘First Monument Commercial Bank’.

Ya yi barazanar bayar da makonni biyu a tsige Adam Nuru ko kuma ya fara kamfen din kaurace wa FCMB daga kwastomomin bankin.

PREMIUM TIMES ta tuntubi Kakakin FCMB Diran Olojo, wanda ya ce su na bibiyar salsalar wannan bahallatsa.

Share.

game da Author